Yadda ake warkewa daga cutar coronavirus

US doctors coronavirus

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

—BBC Hausa

Mamayar da coronavirus ta yi wa kasashen duniya da kuma bayanan da masana kiwon lafiya ke yi kan yadda ake daukarta na cikin abubuwan da suka fi tayar wa da mutane hankali.

Ya zuwa ranar Alhamis 26 ga watan Maris 2020, alkaluma sun nuna ce kusan mutum 500,000 ne suka kamu da cutar a duk fadin duniya yayin da sama da mutum 22,000 suka mutu sakamakon harbuwa da ita.

Wani abin da yake ci gaba da jefa mutane cikin fargaba a kan cutar shi ne bayanan da masana harkokin lafiya suka yi cewa har yanzu ba a samu maganinta ba.

Sai dai duk da wannan mawuyacin hali da coronavirus ta jefa duniya, an soma samun labari mai dadi inda mutanen da suka kamu da ita suke warkewa.

A cewar hukumomi da kuma kungiyoyin da ke bibiyar yaduwar cutar, ciki har da Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka, ya zuwa ranar Alhamis fiye da mutum 120, 000 ne suka warke daga cutar COVID-19 a fadin duniya.

A Najeriya, ranar Alhamis gwamnatin Lagos ta bakin Tunde Ajayi, mai magana da yawun gwamna Babajide Sanwo-Olu, ta ce mutum shida sun warke daga cutar.

Hakan na nufin mutum takwas ne kenan suka warke daga Covid-19 a Najeriya, yayin da mutum daya ya mutu tun lokacin da cutar ta bulla a kasar.

Yaya ake warkewa ganin cewa ba a samar da maganinta ba?

Ko da yake har yanzu ba a samu riga-kafi ko maganin cutar coronavirus ba, amma masana harkokin lafiya sun ce ana warkewa daga cutar idan aka dauki wasu matakai.

Dakta Nasiru Gwarzo wani masanin harkar lafiya ne a Najeriya, ya ce yawancin cutukan da kwayar cutar virus ke haddasawa, ko babu magani, jiki yana iya warkewa saboda suna da wa’adi.

“Idan mai dauke da cuta irin coronavirus ya samu kulawa mai kyau, kamar samun abinci mai sinadaran da ke bunkasa lafiya, da shakar iska mai kyau da motsa jiki, babu shakka zai warke.

Galibin wadannan cututtukan da virus ke haddasawa suna da lokacin fita daga jikin mutum.

Misali, Ebola tana yin kwana 22 a jikin mutum, ita kuma coronavirus tana yin kwana 14, yayin da mura ke yin kwana uku. Idan ka ga mutum bai warke ba, ta ci karfinsa sosai kuma bai samu kulawar da ta kamata ba.”

Ya kara da cewa babu wasu bayanai na kimiyya da ke nuna cewa cutar covid-19 tana sanya wa wanda ya yi fama da ita lalura ta dindindin ko da ya warke.

“Gaskiya har yanzu ana bincike kan coronavirus amma abin da ya bayyana shi ne babu wata hujja da ke nuna cewa irin wadannan cutuka da virus ke haddasawa suna haifar da tawaya ta din-dindin.

Ya danganta da karfin garkuwar jikin mutum da kuma kulawar da ya samu.

Misali, wasu kan yi fama da ciwon kunne ko da kuwa sun warke daga zazzabin Lassa, amma wasu suna warkewa sarai ba tare da fuskantar wata matsala ba, in ji Dakta Gwarzo.

Bayanan da ya kamata ku sani game da coronavirus

Wadanda suka warke suna iya sake kamuwa?

Masanin harkar lafiyar ya ce ba shi da masaniya kan ko wadanda suka warke daga coronavirus na iya sake kamuwa da ita, tun da har yanzu ana bincike.

Amma ya ce idan aka kwatanta da ta cutar shawara, wacce idan mutum ya warke har abada ba zai sake kamuwa da ita ba, to za a iya cewa ita ma coronavirus za a iya warkewa ba tare da an sake kamuwa da ita ba.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...