‘Yadda ake nuwa mana wariya da sunan karin magana’

Hausawa na amfani da karin magana da azancin magana badan-daban domin nuna kwarewa da iya salon zance a yayin magana.

Sai dai a lokuta da dama wasu karin maganar kan ci wa wasu jinsin mutane tuwo a kwarya, domin suna zama tamkar kalaman wariya a garesu.

Irin wadannan karin magana sun hadar da wadanda ake yi da suke sanya masu wata nakasa ko tawaya ta zahiri ko kuma wata koma bayan rayuwa su ji cewa kai tsaye da su ake.

Misali

  • Dinyar makaho ta nuna a hannunsa.
  • Abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa.
  • Kwace goruba a hannun kuturu ba wuya ba ne.
  • Kowa ya ci ladan kuturu zai masa aski.
  • Duk daya ne, makafi ya yi dare.
  • In ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa ya taka dutse.
  • Da haka aka fara kuturu ya ga mai kyazbi.

Duka wadannan karin maganan da azancin maganar an haramta amfani da su a ka’idodjin BBC Hausa, a rediyo ko kuma a rubuce.

Domin guje wa irin wannan saba wa masu bibiyar mu ko sauraren mu a koda yaushe a ko ina a fadin duniya.

A baya-bayan nan a wata tattauna ta musamman da BBC ta yi da wasu makafi sun yi korafin cewa sukan ji ba dadi a lokuta da dama idan suka ji irin wadannan karin magana.

Shugaban kungiyar makafin Najeriya ta sashen Kano, Saifullah Mukhtar ya soki ire-iren karin maganganu da mutane suke yi a kan makafi.

Ya ce irin karin maganar da ake yi kan makafi ba ya sa suna jin dadi. Ya kara da cewa abin cin mutunci ne da nuna bambanci.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...