Ya za ki ji idan ki ka haifi ‘yan biyar lokaci guda?

Jarirai 'yan biyar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya matar ta taba haihuwar tagwaye da ‘yan uku a baya

Wata mata a Uganda ta haifi jarirai biyar ba zato ba tsammani, inda uku daga ciki mata ne yayin da ragowar biyun suka kasance maza.

Tun da farko dai likitoci sun shaida mata cewa tagwaye za ta haifa, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta kasar ta ruwaito.

A baya dai, Sofiat Mutesi wadda ta fito daga kauyen Nawaikoke da ke gabashin kasar ta taba haihuwar tagwaye da ‘yan uku in ji jaridar.

“Na yi mamakin haihuwar ‘ya’ya biyar saboda lokacin da na je aka yi hoton cikin a cibiyar lafiya ta Nsinze, likitoci sun shaida min cewa ina dauke ne da tagwaye,” a cewarta.

An ruwaito cewa tana neman taimako don tallafawa ‘ya’yan nata.

A cewar jaridar Monitor, mijinta na fari ya rasu kuma mijinta na yanzu na da ‘ya’ya 20.

Maureen Babine, wata ungozoma a asibitin Iganga-Nakavule, ta ce mahaifiyar da jariranta na cikin koshin lafiya.

“A duk shekarun da na yi ina aiki a asibitin nan, ban taba ganin matar da ta haifi ‘ya’ya biyar ba. Muna samun ‘yan biyu dai da ‘yan uku… Jariran nata duk sun isa haihuwa, sai dai suna da kankanta kuma suna bukatar kula na musamman,” a cewar malamar jinyar.

[ad_2]

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...