Ya Kamata Najeriya Ta Yi Hankali Da Cin Bashi | VOA Hausa

Najeriya ta cigaba da karbar basuka daga kasashe da kuma kungiyoyi daban daban na duniya domin habbaka sassan kimiya da fasaha da kuma samar da wutar lantarki.

Jimlar basukan dai sun ja hankalin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan inda yayinune akwai bukatar takatsatsan akan sha’anin chiyechiyen bashin da Gwamnatinkeyi.

Sanata Ahmed Lawan ya ba da shawarar a yi takatsantsan din ne a wata sanarwar da wani hadimi a ofishinsa mai suna Ezrel Tabiowo ya raba wa manema labarai .

Shugaban Majalisar ya ce ana fama da karancin arziki wanda ya danganta shi ga rashin tashi tsaye da hukumomin Gwamnati ke yi wajen samowa da kuma mika kudaden shiga ga aljihun gwamnati.

A bisa kiyasin da Shugaba Buhari ya yi a kasafin kudin shekarar 2020, ana kyautata zaton za a sake ciwo wasu basuka wajen aiwatar da kasafin, wanda hakan wani abu ne da Jami’ar majalisar dinkin duniya a ofishin Hukumar Lamuni ta Duniya da ke Najeriya, Aisha Yasmin Zakari, ta ce babu laifi idan an ciwo bashi tunda kasa ta na da kaddarori da abin da za a biya basukan da su. A cewar ta wanan shi ne abin dubawa, saboda kasa tana da kadarorin ta masu yawan gaske.

Majalisar ta sake tafiya hutu daga yanzu zuwa 5 ga watan Nuwamba domin ba Hukumomi da ma’aikatun Gwamnati dama saboda su kamamla bayani akan kasafin kudinsu.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...