Wutar NEPA ta dawo a Najeriya

An dawo da wutar lantarki a Najeriya, bayan da babban layin wutar lantarkin kasar ya mutu da sanyin safiyar Alhamis.

Lamarin ya janyo katsewar wutar lantarki ga kamfanonin rarraba wutar a fadin Najeriya.

Sai dai kuma an dawo da ita ne bayan an shafe sa’o’i da dama ba tare da ita ba a sassan Najeriyar.

Tun da farko dai kamfanin wutar lantarki (TCN) ya tabbatar da rugujewar babban layin wutar a Najeriya, amma kuma ya tabbatar da cewa ana kokarin shawo kan lamarin.

More News

An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro. Mazaunan garin...

Sojoji sun ceto mutane 6 daga cikin É—aliban jami’ar Gusau da aka sace

Sojoji sun ceto dalibai mata shida daga cikin daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da aka bada rahoton yan bindiga sun yi garkuwa da...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da É—aliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a. ‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...