Wutar daji ta jefa Algeria cikin mawuyacin hali

Smoke rises from a wildfire in the forested hills of the Kabylie region, east of the capital Algiers, on August 10, 2021.

Asalin hoton, AFP

Korayen tsaunukan yankin Tizi Ouzou na Aljeriya, masu lulluɓe da lambun zaitun da bishoyi masu cikar ganye, yanzu wutar daji sama da ɗari ta lalata su cikin mako biyu.

Ana iya jin zafin wutar daga wuri mai nisan gaske.

A wani gidan sayar da mai a lardin Bouira, wani mutum mai zuba wa ababen hawa mai ya wahala da yanayi ya sauya ya koma na tsananin zafi.

“Zafin na fitowa ne daga tsaunukan. Ban taÉ“a ganin wutar daji irin wannan ba,” ya shaida mana.

Wutar daji ba sabon abu ba ne a Aljeriya, musamman da yankin arewa maso gabashi na Tizi Ouzou.

A iya cewa ma abu ne da aka saba gani a kai a kai da masu aikin agaji ke fama duk shekara.

Kuma wutar dajin na yin barna mai ɗumbin yawa duba da rashin ruwan sama da iska mai ƙarfin gaske da ke kaɗawa.

Dubban hekta a kusa da ƙauyukan Larbaâ Nath Irathen, Beni Douala da Aït Mesbah ne wutar ta mamaye ta ƙona bishoyoyin masu yawan ganye da a baya suke jere a kan tsaunukan.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Masu aikin agaji na amfani da duk abin da suka samu wurin kashe wutar dajin

Rahotannin farko-farko sun gano cewa wutar ta wannan shekarar ta yi É“arna ga dazukan Algeriya fiye da duka watar dajin da aka yi daga shekarun 2008 zuwa 2020 gaba É—aya.

Aƙalla mutum 90 sun mutu yayin kashe wutar ciki har da sojoji 33 da aka bai wa lambar yabo.

Duk da ƙoƙarin kashe wutar daji duk shekarar, da kuma iƙirarin kasafin kuɗi na sojoji mafi yawa a Afrika, Aljeriya ba ta da jiragen sama na kashe wutar daji.

A maimakon haka, wasu ƴan tsirarun helikwafta ne kirar Mi-26 da ke iya ɗaukar bokiti mai girman lita 1,000 suka yi koƙarin kashe wutar.

Don haka, dole gwamnati ta nemi agaji daga Tarayyar Turai kuma ran 12 ga Agusta, Shugaban faransa Emmanuel Macron ya aika masu da jirage biyu.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,
Helikwaftoci sun yi amfani da manyan bokitan ruwa don kashe wutar

Mutanen ƙauyen Beni Douala sun shiga aikin kashe wutar da shebir da resukan bishiya da duk wani abu da suke da shi.

“Ƙila fasfo É—in sa ne ya lalace,” Fethi Fellah wani dan agaji ya faÉ—a cikin raha lokacin da aka tambaye shi ko ya ga jirgi kashe wuta.

“Baya ga Æ´an kwana-kwana, babu wand aya fito ya agaza mana,” ya ce a lokacin da yake karkatar da jerin motoci daga tsaunukan zuwa birnin Tizi Ouzou inda iyalai suka taru a wasu rumfunan agaji.

ÆŠaya daga cikin wuraren shi ne babban É—akin taron Le Printemps da ke karbvar mutanen da suka tsere daga muhallansu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Mutane da yawa sun tarar gidajensu sun kone ƙurmus

Fuskokinsu sun cika da jajircewa da É“acin rai a lokacin da suka fahimci su za su yi wa kansu komai.

“Hukumomi ba su agaza mana wajen tserewa ba, dole muka dogara da masu aikin sa kai da ke zuwa daga Æ™auye zuwa Æ™auye,” a cewar Ines, wata ma’aikaciyar sa kai.

“Hukumomin na da wani É“angare na alhakin yawan mutanen da suka mutu. Duk shekarar muna samun wutar daji kuma har yanzu ba a É—auki wasu matakai ba,” a cewarta.

Daga Firai Minista Aymen Benabderrahmane da Shugaba Abdelmadjid Tebboune sun ce wasu ɓata gari ne ke sa wutar dajin, sai dai kuma ba su ba da wata ƙwaƙƙwarar hujja kan haka ba.

Sun zarfi ƙungiyoyin ƴan aware a yankin kabyle a kusa da Tizi Ouzou kuma sun ce za su sake duba alaƙar diflomasiyya da Maroko wadda ta ke zargi da goyon bayan ƙungiyoyin.

Sai dai sun manta da cewa ƙasashen da ke kusa da yankin Mediterranean suna fama da wutar daji a makonnin baya-bayan nan ciki har da Turkiyya da Girka da Cyprus da Italiya da Faransa.

Mai yiwuwa sauyin yanayi a yankin da taka rawa wajen faruwar abubuwan da ke janyo wutar dajin.

Sai dai har yanzu É—umamar yanayi ba ya cikin wani batu da ake tattaunawa a Ajeriya.

Kuma asarar rai da ta muhalli da ake samu sanadiyyar bala’o’i sun fara yawan da ba za a iya kauda kai ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
A ƙalla mutum 90 sun mutu suna ƙoƙarin kashe wutar daji

Wutar daji ba ita ce kawai alamar sauyin yanayi a Aljeriya ba.

Hamadar Sahara, wadda ita ce kashi 80 cikin 100 na ƙasar na ƙara girma.

Ta ƙaru da kashi 10 cikin dari a shekaru 100 da suka gabata a cewar mujallar Journal of Climate.

Ƙaruwar hamadar na toshe hanyoyin da makiyaya ke bi don sama wa dabbobi abinci kuma tana tursasa wa manoma ƙara haƙar ƙasa don samun ruwa.

Ga al’ummun da dama can suke daga gefe-gefen hamadar, É—umamar yanayi na Æ™ara jefa su cikin mawuyacin hali musamman a lokacin bazara.

Ɗalibai a lardin Adrar, misali, na cikin rukunin ɗalibai da ke baya-baya a ƙoƙarin makaranta a kasar, saboda ba a gina azuzuwansu don iya zama a lokacin tsananin zafin yankin ba.

A Algiers babban birnin ƙasar, rashin isasshen ruwa ya sa wasu sassan birnin ba sa samun ruwa a famfo sai na ɗan wani lokaci a wuni guda.

Shugaba Tebboune ya sanar da cewa za a samar da tashoshin cire gishiri daga ruwan teku guda uku don shawo kan matsalar.

Sai dai, idan ba a É—auki sauyin yanayi da muhimmanci ba, sannan a sa manufofi kan muhalli, irin waÉ—annan ayyukan za su samar da sauki ne kawai a gajeren zango.

(BBCHAUSA)

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...