Wata mata ta rasu, yara biyu sun jikkata sakamakon ruftawar gini a Kano

Wani gini da ya ruguje a unguwar Makwarari da ke jihar Kano ya lakume rayukan wata uwa ‘yar shekara 35 tare da raunata ‘ya’yanta guda biyu.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya fara a daren ranar Alhamis ya kuma ci gaba da zuwa da sanyin safiyar Juma’a.

Matar mai suna Balaraba Tijjani, tana gida tare da ‘ya’yanta, Abdulnasir da Abdallah, masu shekaru 11 da 13, a lokacin da lamarin ya faru.

A cewar maigidanta Tijjani Magaji, ginin ya ruguje ne saboda tsananin ruwan sama.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ginin wani bene mai hawa daya ne mai tsawon kafa 30 da kafa 40.

Yaran kuwa an kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin kula da lafiyarsu.

More from this stream

Recomended