Wasu matan Indiya sun bayyana dalilin da ya sa suke tsananin son Shah Rukh Khan

  • Daga Aparna Alluri
  • BBC News, Delhi
Shah Rukh Khan a fim din Dilwale Dulhania Le Jayenge

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Khan daya ne daga cikin shahararru a masana’antar Bollywood

“Me ya sa kuke son Shah Rukh Khan?”

Tambayar da na yi wa wasu daga cikin ƙawayena kenan a baya-bayan nan. Tambayar ta ba su mamaki, domin abu ne da ba su zaci zan tambaya ba.

Ni ma a baya ban damu ba, sai da wani sabon littafi ya bayyana yadda ake son ganin Shah Rukh a fujajan, ya sanya ni tunanin me ya sa ake son shi haka.

Sun ce: “kyakkyawa ne” kuma “yana da kirki”, “akwai barkwanci”, “ya dace da abin da yake yi” sannan “akwai nutsuwa”idan an yi masa tambayoyi, kuma “ba ya karaya, kuma ba ya ba da hakuri matukar ya san bai aikata ba daidai ba” uwa uba fitacce ne kuma attajiri.

Da na takura, sai suka fara zurfafa tunani kan fitowar da yake a fina-finai, sai dai suna nuna jin dadi kan ƙaunar da yake nunawa mata soyayya.

“Da gaske ne! mu na son shi, saboda Æ™aunar da yake yi wa mata!” Daya daga cikin Æ™awaye na ta fada min, na yi mamakin hakan sosai.

Wannan shi ne abin da marubuciya Shrayana Bhattacharya ta gano lokacin da ta tambayi gwamman matan da ke ƙaunar Khan.

“Da suna fada min lokaci, da yadda suka fara Æ™aunar shah Rukh, sun shaida mana kan yadda duniya ta kassara su,”kamar yadda Mis Bhattacharya, ta rubuta.

Wannan ba bincike ne da za ai gaggawa a kai ba. An shafe shekaru kusan 20, ana tattaunawa, da Æ™awaye, da ma’aurata, da wadanda ba su da aure tsakanin matan da ke arewacin Indiya.

Akwai mabiya addinin Hindu, da Musulmai, da Kirista, masu farin ciki da akasin haka, da matan da ke cikin matsananciyar damuwa, da mata ma’aikata.

A shekarun 1990 ne Khan ya fara mamayar zukatanmu, cikin tallan kamfanin Coca-Cola da na talbijin, hakan ya fara nuna an fara bude sabon babu a kasar, a daidai lokacin da aka fara sauye-sauyen manufofin bunkasa tattalin arziki.

“Ina son ba da labarin matan da ke tsananin kaunar Khan, da ba safai ake ganin su ba,” in ji Mis Bhattacharya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Mata sun fi yawa a masoyan Khan

Tana duba wani mai yin turaren wuta na tsinke, a wata unguwar marassa galihu da ke yammacin Indiya, a shekarar 2006, a nan ta gano sun gaji da batun mafi karancin albashin ma’aikata.

A lokacin d suke hutawa sai ta fara hira da mutane kan su waye zakarunsu a fannin fina-finai.

“Sun fi mai da hankali, kan Shah Rukh, yadda suke Æ™aunarsa da yadda yake burgesu, da abin da suke son ganin yana yi a cikin fina-finai.”

Tun ba a je ko ina ba, Mis Bhattacharya ta gano bakin matan ya zo daya ba wai a soyayyar Khan ba, har da fafutukar da suke yi a ayyukan da ke kawo musu dari da kwabo.

Duk tunaninsu daya ne, me ya sa mazaje da samari ba za su din ga abin da Shah Rukh ke yi a talbijin ba?

“Suna son kwatanta shi da sauran maza, suna ganin sauran maza na yin abin da Khan yake yi a cikin fina-finai,” in ji Mis Bhattacharya.

Khan yana sadaukar da rayuwarsa kan masoyiyarsa ƙwaya ɗaya jal, da yake ba ta cikakken lokaci, yana da sauraron mace.

Yanayin yadda yake tafiyar da rayuwarsa, da tunain yadda makomarsa za ta kasance nan gaba na daga cikin bin da ke sanya mata kaunar shi.

Yana yawan fitowa a fina-finai cikin nuna soyayya, dalilin da ke nuna baya jin kunyar nunuwa mace abin da ke ran shi da yadda ya ke damuwa da su.

“Ina zan samu wanda zai Æ™aunace ni ko ya taba ni, kamar ydda Khan ya ke yi wa Kajol a cikin fim din Kabhi Khushi Kabhie Gham, na san hakan ba za ta taba faruwa ba.

Mijina kullum cikin jin haushi yake, hannunsa sam babu taushi bare halinsa,” in ji wata matashiyar Musulma, da ke aiki a masaÆ™ar É—inka tufafi.

Wata mace mai kudi, kuma diyar sarauta, ta ce ta na son bai wa ‘ya’yanta tarbiyyar yadda za su zama mazaje na gari.

Yadda za su san yadda ake ji idan ana kuka, su kuma sanya matansu farin ciki kamar yadda Shah Rukh ya ke sanya mu jin soyayya, farin ciki da samun kulawa.

Fim din Dilwale Dulhaniya Le Jayenge na daya daga cikin fina-finan da suka janyowa Khan da masana’antar Bollywood daukaka, da suna, saboda yawanci akan soyyya ne da yadda ake nunawa mace ita.

Sai dai mahaifiyar wata matashiya da ke kaunar Khan ta fada min wani abu da ban taÉ“a yin tunaninki ba: “Shi ne karon farko da na ga yadda jarumin fim, ya ke aikin cikin gida da daukar lokaci yana taya mata aiki a gida.”

A gare ta wannan tsantsr soyayya ce. Ba wai fa wadannan matan ba sa magana akan soyayyar daki ba, suna batu ne kan abubuwa daban-daban.

Karin labaran da za ku so

Asalin hoton, Yash Raj Films

Bayanan hoto,
Khan da Kajol sun fito a fina-finai da dama

Yawancin masoyan shi mata sun fusknci wata matsala lokacin kuruciya, daga wadda mahaifiyarta ta kwadawa mari lokacin ta na karama, saboda satar hanyar zuwa Silima kallon fim din shi.

Sai wadda matashiyar mai aiki a masakar tufafi da ta bai wa yayyenta na goro su rufa mata sirin zuwa kallon fim din Khan da ya fito, da mai aikatau da ta yi wa limamin cocinsu Æ™arya Lahadi hudu a jere kawai, domin zuwa ganin fim dinsa, dadi da ‘yancin da suke samu idan suna kallon fim din ba zai taba misaltuwa ba.

Hasalima yawancin ‘ya’yan talakawa masoyan Khan, ba su taba ganin wasu daga cikin fina-finansa ba, sun dogara ne da jin wakokin fina-finansa.

“Ba abu ne mai sauki ba mata su saurari wakoki, ko kallon fim ko ma kallon tauraron fina-finai,” in ji Mis Bhattacharya. “Idan mace ta ce tana son tauraron fim, ko yana burgeta, ko yadda yake kwalliya, sai a yi mata mummunar fahimta.”

Mis Bhattacharya ta rubuta cewa matan ba wai masu tsattsauran ra’ayi ba ne, amma a kokarinsu na samun farin ciki da nishadi sai ka ga sun yi tawaye.

Sukan boye hotunan Khan karkashin gado, su na sauraro da yin rawar idan suna jin wakokinsa, dan wannan tawayen da suke yi shi ya sanya suka gane ainahin abin da suke bukata a rayuwa wato farin ciki d nishadi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Khan ya fito a fina-finai sama da 100 a shekaru kusan 30 da ya yi a masana’antar Bollywood

Misali ita jami’ar gwamnati, burinta shi ne ta samu ‘yancin yin rayuwar da take so, ba ta bukatar nemin izini kafin ta kalli fim din Khan.

Akwai matashiyar da ta tsere daga gida bayan an tona asirin zuwanta silima kallon fim din Khan ya fito, sakamakon fadan da suka yi da wani da ba ya son shi, har ya kalubalance shi.

(Ko da ya ke daga baya ta samu aiki a cikin jirgi, sannan kuma ta auri mutumin da dabi’u da yadda yake tafiyar da rayuwarsa suka yi kamanceceniya da ta Khan).

Ni da kawayena muna da ‘yancin kallon fim din Khan, saboda babu wanda ya ke kafa mana doka ko tsangwama, babu mai haramta ma na yin wani abu da bai gamsar da mu ba.

Sai bayan na karant littafin, sannan na gane yadda mahaifiyata da yyata suke yin tawayen uwa kallon fim Silima kusan kowacce juma’a, kuma da daddare, sannan na gane sa’ar da na yi da ‘yancin da na samu.

Mis Bhattacharya ta ce Khan ya kawo sauye-sauye a masana’antar Bollywod daga lokacin da ya fara kawo yanu, kuma ya na cin ganiyarsa har yau.

“Ƴan matan ba wai son auren Khan su ke yi ba, kwi so suke yi su zama kamar shi – su na son su daukaka da shahara kamr dai yadda ya samu.”

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...