Wasikar tuhuma: Sarki Sanusi ya mayar wa Ganduje martani | BBC Hausa

Jihar Kano
Image caption

Dangantaka tsakanin gwamnati da masarautar Kano ta kara tsami tun bayan zaben da aka yi a jihar

Majalisar masarautar Kano ta mayar da martani ga wasikar tuhuma da gwmanatin Kano ta aike wa Sarki Muhammadu Sanusi II ta meman ya yi bayani dalla-dalla dangane da zargin kashe sama da Naira biliyan uku bayan ya zama Sarkin Kano.

Martaninin na cikin wata wasika ne da majalisar ta aike wa gwmanati ta ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Kano.

Wasikar tace abin da Sarki Sanusi ya gada a asusun masarautar shi ne Naira biliyan daya da miliyan dari takwas da cas’in da uku.

Wasikar wacce mukaddashin masarautar ta Kano Abba Yusuf ya sanya wa hannu, tace sarkin Kano ba shi ne ke da alhakin yin bayani kan yadda aka kashe kudin masarautar ba, tunda ba shi ne akanta masarautar ba.

Masarautar ta kuma gode wa gwamnati saboda ba ta damar yin bayani kan zargi-zargen da ke kunshe a rahoton na hukumar yaki da cin hanci da rashawa, da ma yin cikakken bayani kan yadda aka kashe kudaden.

A ranar Juma’a ne dai gwamnatin Kano ta hannun sakataren gwamnatin jihar ta aike wa Sarki Sanusi wata wasikar neman bayani da kare kai, kan rahoton da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen al’umma ta mika wa gwamnati, inda ta ba da shawarar a dakatar da sarkin domin a samu damar kammala bincike kan zargin kashe kudin masarautar Kano Naira biliyan uku da miliyan dari hudu ba bisa ka’ida ba, zargin da masarautar ta sha musanta wa.

Shawarar na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ke yin tsami tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar, wacce ta faro tun bayan kammala zaben gwamnan jihar.

To sai dai gwmnatin ta Kano ta tabbatar da cewa a ranar Asabar Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun tattauna a wani yunkurin sulhu da Alhaji Aliko Dangote da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya suka yi, tare da sa hannun fadar shugaban kasa.

Fadar gwamnatin ta Kano tace ba a kai ga kammala sluhun ba, amma dai an fara tattauna wa.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake samun sabani tsakanin gwamnatin Ganduje da Sarki Sanusi kan wasu kalamai ko wasu abubuwa da sarkin ya ke yi da ba sa yi wa gwamnati dadi.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...