Wasanni: Kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na 2019

CAF Award 2019

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF za ta bayyana gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar da babu kamarsa a 2019 ranar Talata.

Cikin guda ukun da za a zabi gwarzon bana sun hada da dan wasan tawagar Algeria da Manchester City, Riyad Mahrez da na Masar da Liverpool, Mohamed Salah da na Senegal da Liverpool, Sadio Mane.

Mane da Salah sun taimaka wa Liverpool ta lashe kofin Zakarun nahiyoyi, kuma Salah na takara karo na uku a jere.

Mahrez shi ne ya ja ragamar Aljeria ta lashe kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda Mane ya taimaka wa Senegal zuwa wasan karshe a 2019.

Haka kuma za a bayyana gwarzuwar ‘yar kwallon Afirka da babu kamarta a 2019.

Wadan da ke takara sun hada da Ajara Nchout ta tawagar Kamaru da kungiyar Valerenga da Asisat Oshoala ta Najeriya Barcelona da ‘yar wasan tawagar Afirka ta Kudu mai taka leda a Beijing Phoenix, Thembi Kgatlana.

Koci-Koci da daraktan tsare-tsare da kyaftin din mambobin tawagogin kwallon kafar Afirka ne za su yi zaben gwarzayen Afirka na 2019.

Za a bayyana wadan da suka yi fice a Afirka a wani biki da CAF za ta gudanar a otal mai suna Hurghada da ke Masar.

Dan kwallon da babu kamarsa a bana:

  • Mohamed Salah (Masar da Liverpool)
  • Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City)
  • Sadio Mane (Senegal da Liverpool)

Macen da ta yi fice a tamaula a bana:

  • Ajara Nchout (Kamaru da Valerenga)
  • Asisat Oshoala (Najeriya da Barcelona)
  • Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu da Beijing Phoenix )

Dan wasan da ya yi kwazo a kungiyar Afirka a bana:

  • Anice Badri (Tunisia da Esperance)
  • Tarek Hamed (Masar da Zamalek)
  • Youcef Belaïli (Algeria da Esperance / Ahli Jeddah)

Matashin dan kwallon da babu kamarsa a Afirka a bana:

  • Achraf Hakimi (Morocco da Borussia Dortmund)
  • Samuel Chukwueze (Najeriya da Villarreal)
  • Victor Osimhen (Najeriya da Lille)

Kocin da babu kamarsa a bana:

  • Aliou Cisse (Senegal – Senegal)
  • Djamel Belmadi (Algeria – Algeria)
  • Moïne Chaâbani (Tunisia – Esperance)

Macen da ta fi yin fice a fagen koci a bana:

  • Alain Djeumfa (Kamaru)
  • Desiree Ellis (Afirka ta Kudu)
  • Thomas Dennerby (Najeriya)

Tawagar kwallon kafa ta maza da ta fi yin bajinta a bana:

  • Algeria
  • Madagascar
  • Senegal

Tawagar kwallon kafa ta mata da babu kamarta a bana:

  • Kamaru
  • Najeriya
  • Afirka ta Kudu

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...