Wani mutum ya rasa ransa a garin gwajin maganin bindiga

Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta kama Timothy Dauda wani mai maganin gargajiya ɗan shekara 19 bisa zargin kashe wani mutum mai suna  Alex Ezekiel lokacin da suke gwajin maganin harbin bindiga da ya bashi.

A wata sanarwar da aka fitar ranar Litinin , Moses Yamu mai magana da yawun rundunar ya ce lamarin ya faru ne a ranar  20 ga watan Agusta a ƙauyen Omumu  dake ƙaramar hukumar Akoko-Edo.

Ya ƙara da cewa jami’an rundunar daga ofishin ƴan sanda na Igarra dake Akoko-Edo ne suka kama wanda ake zargin.

“Wanda ake zargin ya yi iƙirarin shi mai maganin gargajiya ne da ya ƙware wajen haɗa maganin bindiga da adda ko wuƙa,” a cewar sanarwar.

“Wani Alex da yanzu ya mutu yaje wajen mai maganin gargajiyar ya karɓi maganin da aka haɗa masa.

“Bayan an haɗa maganin ne, mai maganin gargajiyar ya yi ƙokarin gwada karfin maganin ta hanyar harbin marigayin.”

Sanarwar ta cigaba da cewa garin haka ne marigayin ya samu mummunan rauni kuma an garzaya da shi asibitin Igarra inda aka tabbatar da mutuwarsa.

More from this stream

Recomended