Wani Dattijo Ya Rataye Kansa Har Lahira

Wani dattijo mai shekaru 80 mai suna Isiyaka Ayinde ya kashe kansa a Watch Tower da ke unguwar Araromi Imota a jihar Legas.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na dare a ranar Alhamis.

Majiyar ‘yan sanda ta shaida wa manema labarai cewa, marigayin ya rataye kansa da igiya a cikin kicin.

“Ya ji ’ya’yansa suna ta ihu cewa ya zo ya ga Baba a kicin. Da gudu ya shiga cikin kicin ɗin, sai ya tarar da gawar dan hayar a rataye a jikin wata igiya,” inji majiyar ‘yan sandan.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar.  , Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended