Walkiya ta halaka shanu jahar Ondo – AREWA News

Akalla shanu takwas walkiya ta kashe a Ekan-Ikale dake yankin Ikare-Akoko a jihar Ondo.

Hakan na zuwa ne wata guda bayan da walkiya ta kashe wasu shanu 36 a Ijare dake karamar hukumar Ifedore ta jihar Ondo.

Shanun sun mutu bayan da suka hau wani tsauni inda basaraken garin yake sadaukar da jini a duk shekara.

Da yake magana akan batun na baya-bayan nan wani mazaunin yankin ya fadawa jaridar The Cable cewa mai makon masu shanun su jefar da su sai suka gasa, suka rika sayarwa da mahauta da basu da masaniyar abin da ya faru.

Amma gwamnatin jihar Ondo ta shiga lamarin inda ta hana sayar da naman shanu a yankin.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...