Wa’adin da ƴan uwan fasinjan jirgin ƙasa da aka sace suka ba gwamnati

‘Yan uwan fasinjan da aka sace a jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna sun ba gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 72 da ta gaggauta kubutar da ƴan uwansu da ke hannun ƴan bindiga.

A wani taron manema labarai da suka kira sun ce idan har gawamnati ta gaza kuɓutar da fasinjojin, za su yi duk abin da ya dace don ganin an sako ‘yan uwansu.

Ƴan uwan fasinjan sun ce sun haɗa kansu suka yi ƙungiya a matsayinsu na ƴan uwan waɗanda aka sace.

A ranar Litinin 28 ga watan Maris, ƴan bindiga suka kai harin bom a jirgin ƙasa da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja suka saci mutane da dama tare kashe mutum takwas.

Aƙalla mutum 68 ake tunanin ke hannun ƴan bindigar. Kuma tsawon mako biyu kenan suna hannun ƴan bindiga.

Me ƴan uwan fasinjan suka ce

Ɗaya daga cikin ƴan uwan fasinjan ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun daina magana da su.

“Tun bayan kwana biyu da abin ya faru suka sanar da mu cewa yan uwanmu na hannunsu ba su sake tuntuubar mu ba,” in ji shi.

Ya kuma ce har yanzu babu wanda ya tuntuɓe su daga ɓangaren gwamnati kan halin da ƴan uwansu suke ciki

“Gwamnatin tarayya da ta Kaduna da ma’aikatar sufuri babu wanda ya tuntuɓe mu ko sanar da mu kan koƙarin da gwamnati ke yi.”

Ƴan uwan fasinjan sun yi kira ga gwamnati ta gaggauta tattaunawa da ƴan bindigar domin a cewarsu “ƴan bindigar a bidiyon da suka fitar sun nuna cewa da gwamnati suke son magana domin ta san abin da suke nufi.”

“Idan har gwamnati ta ƙi, za mu yi duk abin da za mu iya domin kuɓutar da ƴan uwanmu, duk da mun san cewa gwamnati ya kamata ta yi abin da ya dace.

Ƴan bindigar sun yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.

A ranar Laraba ne, wani bidiyo da ya bayyana, ya nuna wasu daga cikin maharan ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan.

Sun kuma sake fitar da wani bidiyo da ke nuna fasinjan suna roƙon gwamnati ta ceto su.

Gwamnati tarayya ta ce ba za ta bayyana ƙoƙarin da ake na tattabatar da kuɓutar da fasinja ba da aka sace, kamar yadda ƙaramin ministan sufuri ya bayyana. Gbemisola Saraki.

More News

Ɗalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...