Unai Emery: ‘Kananan ‘yan wasa suna bukatar a ba su dama’

Mesut Ozil walks off the pitch past Arsenal manager Unai Emery

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau biyu kacal Mesut Ozil ya taka wa Arsenal teda a kakar bana

Kocin Arsenal Unai Emery ya ce bai yi amfani da dan wasan tsakiyarsa Mesut Ozili a wasan da suka doke Standard Liege da ci 4-0 a Gasar Europa ba ne saboda kananan ‘yan wasa suna da bukatar su ma a ba su dama sosai.

Gabriel Martinelli, mai shekara 18, ya zura kwallo biyu a raga yayin da shi ma Joe Willock, mai shekara 20, da kuma Dani Ceballos, mai shekara 23, suka zura kwallo guda-guda.

Yanzu ba a yi amfani da Ozil, mai shekara 30 ba, a wasanni biyu da Arsenal ta buga.

“Ya kamata mu rika ba kananan ‘yan wasa dama,” in ji Emery.

Arsenal ce ta hudu a teburin Gasar Premier kuma za ta fafata ne da kungiyar Bournemouth a ranar Lahadi.

Game da Ozil, Emery ya ce: “Lokacin da na yanke hukunci cewa ba zan yi amfani da shi ba na yi hakan ne saboda sauran ‘yan wasa ma suna bukatar a ba su dama.”

“Ya kamata mu ci gaba da aiki. Gobe za mu yi atisaye da ‘yan wasa wadanda ba su buga wasa ba, kuma ranar Lahadi za mu yi wasa – za mu yanke irin wannan hukunci,” inji shi.

“Fatanmu shi ne mu yi nasara a wasan ranar Lahadi a kan Bournemouth kuma za mu ci gaba da yin hakan a duk wasan da za mu buga,” a cewarsa.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...