UEFA ta fitar da fitattun ‘yan wasa 23 a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa Turai, Uefa ta bayyana ‘yan wasa 23 da suka yi bajinta a gasar Champions League da aka kammala ranar Asabar.

Wadan nan ‘yan kwallon za ta iya fuskantar kowacce kungiya da su daga kowacce nahiya da zarar an bukaci hakan.

Chelsea ce ta lashe kofin Champions League na kakar nan, bayan da ta doke Manchester City da ci 1-0 a Porto, Portugal.

Asalin hoton, Getty Images

Wannan shi ne karon farko da Thomas Tuchel ya lashe Champions League a tarihin sa na mai horar da tamaula.

Paris St Germain ce ta sallami kocin dan kasar Jamus a watan Janairu, ita kuwa Chelsea ta damka masa aikin koci, bayan da ta kori Frank Lampard.

Wannan shi ne karo na biyu da Chelsea ta lashe Champions League, bayan wanda ta dauka a 2011/12 ta kuma taba kai wa wasan karshe da Manchester United ta yi nasara a 2007/08.

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta karkare kakar nan ta Premier League a mataki na hudu a kan teburi duk da rashin nasara da ta yi a wasan karshe a Villa Park.

Saboda haka Chelsea za ta buga gasar Champions League ta badi a matakin mai rike da kofi, kuma wadda ta yi ta hudu a Premier League ta kakar nan.

Haka kuma kungiyar Stamford Bridge za ta buga Uefa Super Cup da Villareal, wadda ta lashe Europa Cup a karon farko a tarihin kafa kungiyar shekara 98.

Asalin hoton, Getty Images

Villareal ta yi nasarar doke Manchester United da ci 11-10 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasan 1-1.

Wannan nasarar da Villareal ta yi ya sa za ta buga Champions League a badi kenan, kuma kungiyoyi biyar ne za su wakilci Sifaniya a gasar kenan.

Kungiyoyin sun hada da Atletico Madrid wadda ta lashe La Liga da Real Madrid ta biyu da Barcelona ta uku da Sevilla ta hudu a teburi da kuma Villareal mai Europa League na bana.

Za a buga Uefa Super Cup tsakanin Chelsea da Villareal cikin watan Agusta a Ireland ta Arewa.

‘Yan kwallo 23 da Uefa ta bayya na Champions League:

  • Thibaut Courtois (Real Madrid)
  • Ederson (Manchester City)
  • Edouard Mendy (Chelsea)
  • Cesar Azpilicueta (Chelsea)
  • Rúben Dias (Man. City)
  • Marquinhos (Paris)
  • Antonio Rüdiger (Chelsea)
  • Ben Chilwell (Chelsea)
  • David Alaba (Bayern)
  • Jorginho (Chelsea)
  • Mason Mount (Chelsea)
  • N’Golo Kanté (Chelsea)
  • Kevin De Bruyne (Man. City)
  • Ä°lkay GündoÄŸan (Man. City)
  • Luka Modrić (Real Madrid)
  • Sérgio Oliveira (Porto)
  • Phil Foden (Man. City)
  • Erling Haaland (Dortmund)
  • Kylian Mbappé (Paris)
  • Robert Lewandowski (Bayern)
  • Karim Benzema (Real Madrid)
  • Neymar (Paris)
  • Lionel Messi (Barcelona)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...