Udinese 1-1 AC Milan: Zlatan Ibrahimovic ne ya farke kwallon

Zlatan Ibrahimovic scoring against Udinese

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Zlatan Ibrahimovic ya fara taka leda a kwararren dan wasa da kungiyar Malmo ta Sweden a 1999

Ranar Asabar AC Milan ta tashi 1-1 a gidan Udinese a wasan mako na 17 a gasar Serie A da suka fafata a filin wasa na Friuli.

Udinese ce ta fara cin kwallo a minti 17 da fara wasa ta hannun, Beto, sai dai daf da za a tashi Zlatan Ibrahimovic ya farke wa Milan.

Hakan ya sa dan wasan tawagar Sweden ya zama na uku da ya ci kwallo 300 a karni na 21 tsakanin manyan gasar Turai biyar.

Mai shekara 40 ya yi wannan bajintar tare da Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo.

Sai dai Udinese ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa tsohon dan wasan Watford, Isaac Success jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Mike Maignan.

Ibrahimovic ya ci kwallo 404 a lik a tarihin tamaularsa har da 16 da ya zura a raga a Malmo ta Sweden da 35 da ya ci a Ajax ta Netherlands da kuma 53 da ya zura a raga a gasar kwallon Amurka ta MLS a kungiyar LA Galaxy.

Manyan gasar Turai biyar sun hada da Serie A ta Italiya da La Liga ta Sifaniya da Premier League ta Ingila da Bundesliga ta Jamus da kuma Ligue 1 ta Faransa.

Ronaldo ne kan gaba a cin kwallaye a lik tsakanin gasar Turai mai 483, sai Lionel Messi mai 475 da muka Ibrahimovic na uku.

Dan kwallon tawagar Sweden na buga wa Milan wasanni karo na biyu a kungiyar, bayan da ya taka leda a Juventus da Inter Milan da Barcelona da PSG da kuma Manchester United daga cikin wadanda ya yi a sana’arsa ta taka leda.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...