Tsugune ba ta kare ba kan nadin mukamai a majalisar Najeriya

Sanata Ahmed Lawan

Sanata Ahmed Lawan ya kayar da Ali Ndume a zaben shuagabancin majalisar

Har yanzu batun nadin mukaman da sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya yi, na ci gaba da tayar da kura a jam’iyyarsa ta APC mai mulkin kasar.

Matasan jam’iyyar ne dai suka kekashe kasa suka ce ba su yarda da yawancin mutanen da ya nada a matsayin masu taimaka masa ba, suna masu cewa ya gaje su ne daga mutumin da ya gada wato Sanata Bukola Saraki.

Hakan ne kuma ya sa Ahmed Lawan ya janye mukamin da ya bai wa Festus Adedayo – a matsayin mai magana da yawunsa.

Ba a gama da wannan ba, kwatsam a ranar Lahadi sai ga mutumin da ya nada domin ya taimaka masa a fannin kafafen sada zumunta na zamani, Olu Onemola, ya ajiye mukamin, yana mai alakanta hakan da ce-ce-ku-cen da nadin ya haifar.

Sai dai daya daga cikin jagororin matasan APC wadanda suke korafi kan wannan batu, Alwan Hassan, ya shaida wa BBC cewa sun gamsu da tattaunawar da suka yi da shugaban majalisar.

”Daman batun da muke yi shi ne, wadannan mutane wato Festus Adedayo da shi Olu Onemola sun yi kaurin suna wajen zagin gwamnatin APC, da kalaman batanci ga Shugaba Muhammadu Buhari da shi kan shi Ahmed Lawan,” inji Alwan Hassan.

Karin nadin mukamin mutane biyar da shugaban majalisar ya kara yi, ya sake fusata matasan jam’iyyar ta APC wadanda suke ganin ba su cancanta ba saboda zargin suna sukar gwamnati.

Ya kara da cewa ”Shi kan sa Ahmed Lawan bai san da batancin da suke wallafawa a shafin Twitter ba kan shugaban kasa sai a yanzu da aka nuna masa… Majalisa ta ‘yan Najeriya ce babu dan APC ko PDP ko wata jam’iyya, amma su wadannan suna zagin shugaban kasa ne”.

Sai dai anasa bangaren, Festus Adedayo, wanda fitaccen dan jarida ne, ya wallafa wani sharhi a shafin Premium Times, inda ya ce ba shi “ya nemi mukamin ba tun asali, kuma ba zai taba sauya matsayinsa kan yadda yake kallon al’amuran yau da kullum a Najeriya ba”.

Za dai a zuba ido dan ganin yaya zaman majalisar da ci gaba da nade-naden mukaman za su kaya a makon nan, wanda wasu ke ganin ya kamata wadanda suka yi wa jam’iyya halacci su zamo a sahun gaba a mukaman.

Ya yin da wasu kuma ke batun a duba cancanta ba tare da la’akkari da ‘yan jam’iyya mai mulki ko ‘yan hamayya ba.

Ahmed Lawan ya shafe shekara 20 a majalisar tarayya

Ahmed Lawan ya shafe shekara 20 a majalisar tarayya

Tun da farko dai Sanata Lawan ya fara ne da kokarin kare kansa bayan da wasu kafafen yada labarai suka lakaba masa wani labari da ke cewa ya nemi jam’iyyar APC da Shugaba Buhari da su mika mulki ga yankin Arewa maso Yamma a shekara ta 2023.

Wannan ta sa sai da ya fito ya karyata labarin, inda ya ce wani takwaransa ne, wato sakataren APC na jihar Adamawa, ya yi maganar ba shi ba.

Wani jigo a jam’iyyar APC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ganin irin ja-in-jar da aka yi kan takararsa da yadda ta ja hankalin ‘yan kasar, wani zai yi tunanin cewa Ahmed Lawan zai yi taka-tsantsan a duk irin abubuwan da zai yi.

“Amma abin mamaki sai ga shi ya fara wa’adin nasa da haifar da rudani. Muna fatan ba za a sake maimaita irin wannan ba,” a cewarsa.

Kawo yanzu dai ba a nada wanda ko wacce za ta maye gurbin Mista Adedayo ba, sai dai da alama ‘yan APC za su zura ido domin ganin mutumin da za a nada a karo na biyu.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...