
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Rome inda zai halarci bikin nada sabon Fafaroma Leo XIV a matsayin jagoran mabiya cocin katolika na duniya.
A cikin wata sanarwa ranar Asabar, Bayo Onanuga mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Tinubu yaje birnin Rome ne domin girmama gayyatar da aka yi masa ta taron.
Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman sojoji na Mario De Bernardo da misalin karfe 06:00 na yamma inda ya samu tarba daga karamar ministar harkokin waje ta Najeriya, Bianca Odumegwu Ojukwu, jami’an fadar Vatican da kuma wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya.
Tawagar shugaban kasar ta hada da wasu manyan limaman cocin katolika a Najeriya suka hada da Matthew Kukah, Lucius Ogorji da Alfred Martins