Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya biyo bayan ziyarar makonni biyu da ya kai birnin Paris na kasar Faransa.
Tinubu ya ziyarci birnin ne a wata ziyara ta kashin kansa da ya kai.
Shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 09:00 na daren ranar Talata a cikin jirgin shugaban kasa.
Ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.