Tinubu na yin taron sirri da gwamnoni

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu na  gudanar da wata ganawa ta sirri gwamnonin jihohia a  fadar Aso Rock dake Abuja.

Taron ganawar na zuwa ne bayan da shugaban ƙasar ya gana da shugabannin kungiyar ƙwadago kan tattaunawar da ake ta mafi ƙarancin albashi.

Tun da farko wakilan kungiyar ƙwadago ta NLC da TUC sun gana da shugaban ƙasar a fadar Aso Rock.

Duk da cewa shugabannin kungiyar ƙwadagon da wakilan gwamnati sun bayyana cewa sun tattauna ne akan mafi ƙarancin albashi inda suka ce za su sake gudanar da wata ganawar bayan mako guda.

Sama da wata guda kenan da suka wuce wakilan gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma na kamfanoni masu zaman kansu su ke tattaunawa kan yadda za a samar da mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

More from this stream

Recomended