Tilasta rigakafin corona ga ma′aikata Google da Facebook | Labarai

Kamfanonin guda biyu sun dauki wannan mataki ne ba tare da shawarartar juna ba, sai dai kamfanin google ya ce dokar za ta shafi ma’aikatantan ta da ke Amirka ne kadai a yanzu kamin daga baya a fadada dokar zuwa sauran yankuna a watanni masu zuwa.
Matakin tilasta ma’aikata allurar na zuwa ne sakamakon yaduwar sabon nau’in annobar corona mai suna DELTA, sai dai google na jan kafaka na dawo da ma’aikata aiki a ofis har zuwa tsakiyar watan Oktoba. Amma kamfanin apple na kan bakanta na barin ma’aikatanta su cigaba da aiki daga gida, kuma babu niyyar tilasta ma’aikata yin allurar rigakafin corona.

More News

Ɗalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...