Thank you Buhari: ‘Yan Najeriya na yi wa Buhari godiyar shaguɓe

Buhari

Bayanan hoto,
An kashe fiye da mutum 130 a rana guda a jihohin Borno da Katsina da Adamawa

Masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya musammman wadanda suka fi amfani da shafin Twitter sun wayi garin Litinin da wani maudu’i mai jan hankali da ya shafi shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Maudu’in kuwa shi ne #ThankYouBuhari, wato godiya ga Buhari.

Wannan maudu’i ya kasance mai jan hankali saboda ba kasafai ‘yan Najeriya, musamman matasa da ke kukan matsaloli daban-daban, suke ware lokaci wurin yaba wa shugabanninsu.

Sai dai da mutum ya duba abubuwan da ake fada game da maudu’in zai ga cewa a zahiri shagube suke yi wa shugaban na Najeriya maimakon yabo.

Jam’iyyar APC mai mulkin kasar da ma Shugaba Buhari sun karbi mulki ne a 2015 bayan sun kayar da Shugaba Goodluck Jonathan, wanda shi ne karon farko da jam’iyyar hamayya ta kayar da mai mulki a kasar.

A wancan lokacin, ‘yan kasar na kokawa kan matsaloli daban-daban da suka hada da rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan Boko Haram da tsadar rayuwa da kuma cin hanci da rashawa.

Hakan ne ya sa Janar Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC suke yi wa ‘yan kasar alkawura da dama na inganta rayuwarsu.

Sai dai bayan kwashe fiye da shekara biyar gwamnatin Buhari tana mulki, ‘yan kasar na ci gaba da korafi musamman kan yadda suka ce an samu karin tabarbarewar harkokin tsaro, da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da makamantasu.

Shi ya sa ma a sakonnin da suka wallafa a Twitter kan shugaban na Najeriya, maimakon godiya, ‘yan kasar sun rika yi masa shagube da Allah-wadai kan abin da suka kira “rashin cika alkawuran” gwamnatinsa.

Wasu daga cikinsu sun bayyana shagubensu ne kan yadda Shugaba Buhari ya gaza magance matsalar tattalin arziki:

Dr Penking, wani mai amfani da Twitter, ya soki shugaban bisa rashin cika alkawarin bayar da abinci sau daya ga kowanne dalibi

Shi kuwa Seo9ja ya ce matsalar rashin aikin yi ta kai intaha lokacin Shugaba Buhari, yana mai cewa a 2015 kashi 4.3 ne ba su da aikin yi amma yanzu kashi 33.5 ne ba su da aikin.

Batun tsaro dai na ci gaba da ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya musamman yadda ‘yan bindiga suke kakkashe mutane a arewa maso yammacin kasar, ciki har da jihar Katsina, mahaifar Shugaba Buhari.

Hasali ma, wasu daga cikin masu yi wa shugaban shagube sun bayyana mamakinsu kan yadda gwamnatinsa take yafe wa mayakan Boko Haram sannan ta ba su ayyukan yi, duk da kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu, kamar yadda Paul ke cewa:

Shi kuwa Diekolola Omo Oolore ya yi wa shugaban kasar shagube ne kan yadda kawar da kungiyar Boko Haram sannan ya sha alwashin gano Dadiyata”, wato matashin nan da aka sace a gidansa da ke Kaduna fiye da shekara daya da ta wuce.

Masu lura da lamura na ganin masu amfani da Twitter suna wannan shagube ne saboda dawowa daga rakiyar shugaba Buhari da kuma yadda suka gaji da alkawura da ya kwashe fiye da shekara biyar ana yi musu na inganta rayuwarsu.

A cewarsu, duk da ikirarin da shugaban kasar yake yi na kawo sauyi mai inganci a Najeriya, galibin ‘yan kasar na ganin ba ta sauya zani ba.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...