Thank A Soldier: Sojojin Najeriya suna shan yabo a shafin Twitter

Sojojin Najeriya
Bayanan hoto,
An kashe sojoji da dama a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram

Masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara musamman shafin Twitter sun wayi gari suna yaba wa sojojin Najeriya musamman wadanda ke fagen daga.

Suna yin wannan yabo ne a yayin da kasar ke bikin ranar tunawa da gwarazan sojojin da suka mutu a yakin basasar da aka kwashe wata 30 ana yi a kasar, wanda ya zo karshe ranar 15 ga watan Janairun 1970.

Najeriya ta tsunduma yakin basasa ne bayan da tsohon shugaban mulkin sojin tsohuwar shiyyar gabashin kasar, Laftanar Kanar Chukwuemeka “Emeka” Odumegwu-Ojukwu ya ayyana ballewa daga kasar a shekarar 1967.

Sai dai gwamnatin mulkin sojin kasar ta wancan lokaci karkashin Janar Yakubu Gowon ta yi fatali da shirin ballewarsu inda kasar ta tsunduma yakin da ya yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane cikinsu har da sojojin da suka fafata a yakin.

Hakan ne ya sa aka aka ware kowacce ranar 15 ga watan Janairu, wadda kuma ta zo daidai da ranar da sojoji suka yi juyin mulkin farko a kasar, domin yaba wa sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu domin ganin Najeriya ta ci gaba da zama kasa guda.

Baya ga haka, ana bikin wannan rana ce domin nuna godiya ga sauran sojoji da suke yaki da kungiyoyi irin su Boko Haram domin wanzar da tsaro a kasar.

Abin da ‘yan Twitter suke cewa

Masu amfani da shafin Twitter sun mayar da hankali a wannan rana wajen nuna irin kwazon sojojin Najeriya a lokuta daban-daban wajen tabbatar da zaman lafiya.

Hakan ne ma ya sa mau’idin #ThankASoldier, wato a gode wa soja, da #ArmedForcesRemembranceDay, Ranar Tunawa da sojin da suka mutu, suka kasance wasu daga cikin manyan abubuwan da aka fi tattaunawa a shafin Twitter.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya yi addu’ar Allah Ya jikan sojin da suka rasa rayukansu a fagen yaki.

“Muna da dukkan dalilai da suka kamata mu gode wa sojinmu da suka mutu saboda abubuwan da suka yi da kuma wadanda suke ci gaba da yi domin wanzar da tsaron rayukanmu da kasarmu,” a cewar Atiku.

A nasa bangaren, Akin Wale, ya yaba wa sojojin da aka kashe a fagen yaki musamman fitaccen sojan nan da mayakan Boko Haram suka kashe, Kanar Muhammad Abu Ali.

Shi kuwa Salim cewa ya yi a yayin da “muke gida tare da iyalanmu muna nuna kauna ga juna, amma soji ya sadaukar da kansa ya bar gidansa, iyalinsa da abubuwa da dama domin su kare mu da kasarmu.”

(BBC Hausa)

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...