Sokoto: An Kai Hari Ranar Sallah a Sabon Gari


A daidai lokacin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke shagulgulan sallah karama, al’ummomi a yankin karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto a arewacin Najeriya suka fuskanci wani tashin hankali.
A cewar wasu wadanda suka sheda harin mahara sun fito ranar sallah dauke da bindigogi, suka rinka harbin mutane.
Saboda tsananin harin, sai da aka dukkufa wajen tsintar gawarwaki na mutanen da ‘yan bindigan suka kashe.
Wani wanda ya sheda aukuwar lamarin, ya sheda wa Muryar Amurka cewa, “mutanen sun fito ne daga cikin wani daji wanda ke tsakanin Sabon Birni da garin Bature, inda suka hana kowa wucewa.
“Da muka lissafa gawarwakin mutanen da aka kashe, muna kan 14 a yanzu.”
Yayin da yake tsokaci kan harin, Kwamishinan tsaro a jihar ta Sokoto, Kanar Garba Moyi mai ritaya ya ce “maharan suna karanta yadda ake tsara wuraren da ake aika sojoji.”
“Ba zai yi wu a ajiye sojoji a kowanne kauye ba, suna lura da yadda sojojin ke tafiya daga kauye-kauye ne kafin su yanke shawarar inda za su kai hari.”
A cikin ‘yan kwannakin nan yadda ake kai hare-hare a yankin na kara kaimi.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...