Sojojin Saudiyya za su fuskanci shari’a kan yakin Yemen | BBC Hausa

A Yemeni boy receives treatment at a hospital following a Saudi-led coalition air strike on a bus in Dahyan, Saada province, on 9 August 2018

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A kalla yara ‘yan makaranta 29 ne suka mutu a wani hari da rundunar sojin hadakar ta kai ta sama kan wata motar bas a Dahyan a 2018

Rundunar sojin hadaka da saudiya ke jagoranta a Yemen ta ce ta fara sauraron kararraki kan dakarunta da ake zargi da karya dokokin kasa da kasa da ke kare hakkin dan adam.

Mai magana da yawun rundunar Kanal Turki al-Maliki ya ce za a sanar da hukuncin da aka yanke a shari’o’in da ba a bayyana maudu’insu ba da zarar an kammala.

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun ce za a iya samun rundunar hadakan da laifukan yaki.

Sun kuma bayyana damuwa a kan ‘yancin gashin kai na sashen da rundunar hadakan ta samar don nazarin zarge-zargen karya dokokin.

Yemen ta fara fuskantar yakin da ya ta’azzara a watan Maris din 2015, lokacin da ‘yan tawayen Houthi suka kwace iko da mafi yawan yammacin kasar suka kuma tursasawa Shugaba Abdrabbuh Mansour tserewa daga kasar.

Bayan da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen Larabawa bakwai suka farga da bunkasar wata kungiya da suka yi amannar Iran na goyawa baya, sai suka fara wata fafutuka da nufin dawo da gwamnatin Mista Hadi.

Majalisar Dinkin Duniya ta tantance mace-macen a kalla fararen hula 7,500, wadanda da yawan su hare-haren sama na rundunar hadakan ne suka yi sanadin su.

Wata kungiya da ke sa ido ta kiyasta cewa yakin ya kashe mutum 100,000, da suka hada da fararen hula 12,000.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...