‘Sojojin Najeriya sama da 350 za su ajiye aikinsu’

Sojojin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sojojin Najeriya fiye da 350 za su ajiye aikinsu na soja saboda sun gaji da aikin bisa wasu dalilai na rashin gamsuwa da shugabancin rundunar sojin da kuma rashin karfafa masu ƙwarin guiwa.

Haka kuma ƙarancin albashi da rashin kayan aiki na daga cikin batutuwan da ƙananan sojojin da ke faɗa da Boko Haram suka koka akai.

Mai fafutikar kare haƙƙin bil’adama kuma mai bincike kan Ć™ungiyar Boko Haram Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa akwai wasu Ć™arin sojojin ma da ke son barin aikin na soja amma har yanzu ba a amince da buĆ™atarsu ba.

A baya, rundunar sojin Najeriya ta dakatar da ba sojoji damar yin ritaya a duk lokacin da suka nema inda ake zargin wasunsu da zama matsorata da kuma yin zagon ƙasa yayin da suke sukar shugabancin rundunar sojin.

Sojojin na Najeriya za su ajiye aikin ne a farkon watan Janairun badi.

An shafe shekaru 10 Najeriya na fama da rikicin Ć´an ta’adda na Boko Haram. Kuma rundunar Sojiin Ć™asar ta sha iĆ™irarin cewa ta murĆ™ushe ayyukan Ć™ungiyar amma kuma galibi a É“angarenta ba ta cika bayyana irin giriman hasarar da ta yi ba.

Amma a zahiri maharan na ci gaba da da kai hare-hare kan sojoji da fararen hula, inda a farkon wannan makon aka bayar da rahoton cewa sojoji sama da 30 ne aka kashe a wani harin kwantan É“auna na Boko Haram.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...