Sojojin Faransa 13 sun mutu a hatsarin jirgi a Mali | BBC news

French armoured vehicles seen on patrol in northern Burkina Faso
Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

A shekarar 2013, Faransa ta tura dubban dakarunta Mali bayan da masu da’awar jihadi suka kwace wasu manyan yankunan arewacin kasar

Sojojin Faransa 13 ne suka mutu a yayin da wasu jiragen helikwafta biyu suka yi taho-mu-gama lokacin da suke kai wasu hare-hare kan masu tayar da kayar da baya a Mali, a cewar ofishin shugaban Faransa.

Hatsarin ya faru ne a ranar Litinin da yamma, a cewar wata sanarwa daga ofishin shugaban kasa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin.

A shekarar 2013, Faransa ta tura dubban dakarunta Mali bayan da masu da’awar jihadi suka kwace wasu manyan yankunan arewacin kasar.

Tuni dai sojojin Mali suka kwato yankunan amma yankin na ci gaba da fuskantar rashin tsaro, kuma tashe-tashen hankula sun yadu a wasu sassan kasar.

A yanzu akwai sojojin Faransa 4,500 da aka tura Mali da Mauritaniya da Nijar da Burkina Faso da kuma Chadi, don taimaka wa dakarun kasashen a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya.

Shugaba Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Wadannan sojojin 13 sun mutu da buri daya ne, shi ne kokarin kare mu. Ina taya ‘yan uwansu da masoyansu alhini.”

A farkon watan nan ne aka kashe wani sojan Faransan Birgediya Ronan Pointeau, bayan da aka dasa bam a kusa da motarsa.

Lamarin da ya faru ranar Litinin din shi ne mafi muni na asarar rayuka da Faransa ta fuskanta tun bayan da ta fara shiga tsakani a Mali.

Sojojin Faransa 38 ne suka mutu a jumulla a Mali tun shekarar 2013.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...