Sojoji sun yi ikirarin hambarar da gwamnatin Bazoum a Nijar

Sojoji sun yi ikirarin hambarar da gwamnatin Nijar bayan wani juyin mulkin da aka yi a yammacin Afirka ranar Laraba lokacin da jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka tsare shugaba Mohamed Bazoum.

Majiyar fadar shugaban kasar ta bayyana cewa, mambobin masu gadin shugaban kasar sun rufe kofar shiga gidan shugaban da ofisoshinsu da ke Yamai babban birnin kasar, kuma bayan da tattaunawar ta tsaya, “sun ki sakinsa”.

Sojojin sun ce za a dakatar da “dukkan cibiyoyi” a kasar, a rufe kan iyakoki da kuma sanya dokar ta-baci “har sai an samu sanarwa” daga karfe 10 na dare zuwa 5 na safe.

“Mu da jami’an tsaro… mun yanke shawarar kawo karshen mulkin shugaba Bazoum,” in ji Kanar-Manjo Amadou Abdramane a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin da yammacin Laraba.

More from this stream

Recomended