
Dakarun soja da suka fito daga barikin sojojin ta Zuma dake garin Suleja a jihar Niger sun buɗe hanyar Abuja zuwa Kaduna motoci su cigaba da wucewa bayan da masu zanga-zanga suka tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a hanyar har tsawon sama da awanni biyar.
Wani mazaunin birnin tarayya Abuja mai suna Abubakar Ibrahim wanda yake kan hanyar zuwa Kaduna a motar haya ya ce jami’an tsaron su fatattaki masu zanga-zangar da misalin ƙarfe 03:30 na rana.
Ibrahim wanda ya isa wajen a cikin wata motar haya da misalin ƙarfe 10 na safe ya ce an cire shingen da masu zanga-zangar suka saka ne bayan da suka hana wani babban jami’in soja dake sanye da kayan gida wucewa tare da jerin motocinsa.
Hakan yasa ya juya cikin fushi inda bayan wani ɗan lokaci sojoji suka iso wurin suna harbin iska abun da ya tilastawa masu zanga-zangar tserewa.
Wasu ƙarin rahotanni sun bayyana cewa wani mutum da aka ɗauko za a kai shi asibiti ya rasa ransa a cikin cinkoson motocin da ya faru .