Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 7 a Kaduna

Dakarun sojojin Najeriya da ke aiki ƙarƙashin ‘Operation Whirl Punch’ sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 7 a kauyen Kampanin Doka da ke karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna.

Wannan farmaƙin, wanda aka gudanar a matsayin martani ga hare-haren da ake kai wa al’ummar yankin, ya yi sanadin kakkaɓe ‘yan bindiga hudu a ranar 1 ga Nuwamba, 2023.

A cewar Laftanal Kanal Musa Yahaya, mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya na Kaduna, sojojin tare da hadin gwiwar runduna ta daya ta Najeriya, sun yi gaggawar mayar da martani kan rahotannin hare-haren ‘yan bindiga a kauyen Kampanin Doka.

Rundunar ta kai ga ƙwato makamai da suka haɗa da bindiga kirar AK 47 guda daya, gidan harsasan AK 47 daya, adda daya, wayar hannu, da babura goma sha hudu da masu laifin ke amfani da su a baya.

More from this stream

Recomended