Sojoji Sun kashe Mayaƙan Boko Haram 3 Tare Da Ceto Mutane 9

Dakarun sojan Najeriya na rundunar, Operation Haɗin Kai sun kashe mayaƙan Boko Haram uku a ƙaramar hukumar Bama dake jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama wani masani dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce an kashe mayaÆ™an ne lokacin da sojoji suke gudanar da aikin sintiri.

Ya ce an kashe Æ´an ta’addar ne a Æ™auyen Churchur a yayin musayar wuta lokacin da sojojin suke sintiri.

A wani farmakin na daban sojojin sun samu nasarar ceto mutane 9 da suka haɗa da mata uku da ƙananan 6 s sun kuma lalata sansanin mayaƙan na Boko Haram bayan da suka tsere.

Hakan na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da sojoji suka kashe wasu mutane uku a wani samame da suka kai maɓoyar Boko Haram da kuma mayaƙan ISWAP a jihohin Borno da Katsina

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...