Sojoji a Lagos sun kama wanda ake zargi da kashe shugaban Fulani a jihar Filato

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama Philip Gokas wanda ake zargi da kisan Adamu Gabdo wani shugaban al’ummar Fulani a jihar Filato.

A ranar 23 ga watan Satumba ne aka kashe Gabdo wanda shi ne Arɗon Fulani na Panyam dake karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Kwanaki bayan kisan, Taoreed Lagbaja babban hafsan sojan Najeriya ya bawa jami’an rundunar samar da tsaro a jihar Plateau ta Operation Safe Haven da su kamo wanda suka kashe Gabdo.

A wata sanarwa ranar Laraba rundunar sojan Najeriya ta ce jami’an rundunar Opera Safe Haven sun gano wanda ake zargi a yankin Ogba dake jihar Lagos bayan shafe makonni suna farautarsa.

A cewar sanarwar an kama Gokas ne yana shan giya a wani wurin kallon wasan kwallon kafa.

Rundunar sojan ta ce wanda ake zargi ya amsa laifin kisan Gabdo.

More from this stream

Recomended