Sojin Najeriya ne ke kawo tsaiko a yaki da Boko Haram – Buratai

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Boko Haram ta kashe mutum 30 a Konduga ranar Lahadi. Akwai hotuna masu tayar da hankali

Hafsan sojojin kasa na Najeriya ya dora alhakin tsaikon da ake da ake samu a yakin da kasar ke yi da ta’addanci ga sojojin kasar da ke fagen daga.

Laftanar Janar Tukur Buratai ya zargi sojojin da rashin mayar da hankali domin kare kasar a dukkan ayyukan da umarce su da su yi, lamarin da ya ce abin takaici ne.

“Magana ta gaskiya ita ce za a iya alakanta duk wani koma-baya da muka samu a baya-bayan nan a ayyukan da muke yi da rashin mayar da hankali da nuna kaimi wurin bin umarnin da aka bayar ko ayyukan da aka tsara”.

A takaice za a iya alakanta hakan da rashin nuna halin ko-in-kula da dakarun da suke filin daga suke nunawa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito shi yana cewa a wurin wani taron ranar Talata.

Sai dai wani jami’in soji ya shaida wa BBC cewa kalaman na shugaban nasu “ba su da tushe, yana mai cewa idan ba a yaba musu ba, to bai kamata a tsine musu ba”.

Fiye da shekara 10 ke nan dakarun Najeriya na fafatawa da mayakan Boko Haram a arewa maso Gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 30,000, yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhallansu.

Janar Tukur Buratai ya shafe shekara hudu yana jagorantar rundunar sojin Najeriya

Manyan jami’an sojoji da kanana da dama sun rasa rayukansu a yakin, wanda gwamnati da sojoji suka ce sun ci karfinsa.

Sai dai har yanzu kungiyar na kai hare-hare, inda ko a ranar Lahadi sai da suka kashe mutum 30 a wani harin kunar bakin-wake, yayin da wasu 40 suka jikkata.

Masu sharhi na ganin irin wadannan kalamai na nuna gazawa ne daga bangaren shugabannin sojin, wadanda wasu da dama suke zarga da kasa yin katabus wuirn kawo karshen kungiyar ta Boko Haram duk da makudan kudaden da ake ware musu.

Baya ga Boko Haram, Najeriya na fuskantar matsalar ‘yan bindiga a arewa maso Yamma da masu satar mutane domin karbar kudin fansa a sassan kasar daban daban.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...