Ana zargin jami’an sojoji da harbe, Halliru Liman DPO É—in Æ´an sanda na Wasagu dake jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a wurin wani shingen binciken ababen hawa a jihar Zamfara.
A wata sanarwa ranar Alhamis, Yazid Abubakar mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara ya ce DPO É—in na kan hanyarsa ne ta zuwa Birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi inda zai halarci taron wata wata.
Abubakar ya ce duk da cewa ya bayyana kansa a matsayin ɗan sanda hakan bai hana sojan dake aiki da rundunar samar da tsaro ta samar da tsaro ta Operation Hadarin Daji shiya ta 6 a jihar Zamfara harbinsa a kai ba.
Ya ce lamarin da ya faru har ta kai ga kisan gilla abun damuwa ne kuma baza a amince da shi ba.