Shugabar Myanmar za ta sake gurfana a kotu kan zargin kisan Musulmi

Aung San Suu Kyi

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Aung San Suu Kyi ta musanta zargin cewa kasarta ta yi wa Musulmin Rohingya kisan kiyashi

A ranar Alhamis din nan kotun duniya za ta yi zama na uku kuma na karshe na jin bahasi a karar da kasar Gambia ta kai hukumomin Myanmar, ta zargin yi wa Musulmi tsiraru ‘yan kabilar Rohingya.

Jagorar kasar ta Myanmar Aung San Suu Kyi za ta sake gurfana a gaban kotun, a zaman yayin da inda lauyoyinta za su yi kokarin gamsar da alkalan kotun da kada su yanke hukunci a kan kasar tata.

A yayin zaman kotun duniyar na yau lauyoyin kasar Gambia, da ke Yamacin Afirka, kasar da ta shigar da karar.

Domin ganin kotun ta kare tare da bi wa Musulman ‘yan Rohingya hakkinsu, lauyoyin za su gabatr wa alkalai cewa ‘yan kabilar 600,000 wadanda har yanzu suke zaune a jihar Rakhine ta kasar ta Myanmar suna fuskantar hadarin yi musu kisan kiyashi, daga hukumomin kasar ta Myanmar.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Abin kawai, da zai hana alkalan kotun ta duniya, su 17, yanke hukunci a kan Myanmar din kawai shi ne, idan sun ga cewa batutuwa da kuma wannan neman kariya ga sauran Musulmin ‘yan Rohingya da Gambiyar ke cewa suna cikin hadarin kawar da su daga doron kasa, a hannun hukumomin kasarsu, Myanmar bai gamsar da su ba, har su yi hukuncin da kasar ta Afirka ta Yamma k enema.

A jiya Laraba, jagorar ta Myanmar, Aung Sang Suu Kyi ta amince cewa sojojin kasar tata sun kasha farar hura a 2017.

Amma ta ce sojojin sun yi hakan ne a martanin da suka yi na kokarin murkushe mayakan sa-kai ‘yan Rohingya da ke kai hare-hare, amma ba wai cewa a kwai wani shiri na musamman ba ne na kai wa alummar ta Rohinjawa gaba daya hari ba.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kotun duniya ta ICJ

Kotun duniyar dai ba ta da damar tilasta hukuncin da za ta iya yankewa a kan Myanmar, amma dai hakan kai ya kara damar sanya wa kasar takunkumi, amma zai kara karfin kiran da wasu kasashe da hukumomi ke yi na yi wa alummar Musumlin ‘yan Rohinja adalci.

A baya dai masu bincike na Majalisar dinkin Duniya sun a rahotonsa kan zargin kisan na Musulmi, sun ayyyana cewa sojojin Myanmar sun yi abin da suka yi da niyyar kisan kiyashi, a lokacin murkushe ‘yan Rohingyan, shekara biyu da ta wuce, abin da ya tilasta wa Musulmai 700,000 tsere wa zuwa cikin yankin Bangladesh:

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...