Shugaban kasa zai daukaka kara kan sukarsa da wuka

The moment Jair Bolsonaro was stabbed at rally

Kotu ta saki mutumin da ya soka wa shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro wuka lokacin yakin neman zabe a watan Satumbar bara, bayan wani alkali ya yanke hukuncin cewa yana da tabin hankali.

Ba za a iya yi wa Mista Adélio Bispo de Oliveira shari’ah a karkashin dokokin Brazil ba, saboda ba shi da cikakkiyar masaniya kan abubuwan da ya aikata a lokacin, alkalin tarayyar ya yanke hukunci.

Sai dai ya ce Mista de Oliveira na da “matukar hatsari” don haka ya daure shi tsawon wani maras iyaka ta yadda zai samu kulawar likitoci.

Shugaba Bolsonaro ya ce zai yi kokari ya ga an soke hukuncin.

“Zan tuntubi lauyana. Zan yi kokari na ga na yi duk abin da zan iya,” ya fada wa kofofin labarai ranar Juma’a.

Shugaban wanda sai da aka yi masa aiki bayan faruwar lamarin, ya nuna cewa siyasa ce ta sa aka kai masa harin, kuma wasu mutane ne suka kitsa al’amarin, ba kawai Mista de Oliveira ba.

“Sun yi kokarin kashe ni. Ina da tabbacin ko su wane ne, amma ba zan bayyana su ba, Ba na son yin riga mallam…” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Wannan laifi ne a kan dan takarar shugaban kasa wanda a yanzu yake da ikon mulki don haka sai mun bi kadin wannan magana.”

Sakin mutumin ya zo ne tsawon makwanni bayan wani alkali ya yanke hukuncin cewa an mayar da Mista de Oliveira gidan kula da masu tabin hankali.

Me ya faru ga shugaban?

Mista Bolsonaro, mai shekara 64, ya ji wani mugun rauni a ‘ya’yan hanjinsa da ya zama barazana ga rayuwarsa kuma ya rasa jininsa har kashi 40% lokacin da aka caka masa wuka a ciki yayin wani gangamin yakin neman zabe a Minas Gerais cikin watan Satumban bara.

An kai dan siyasar mai tsananin kishin kasa bangaren masu bukatar matsananciyar kulawa, inda aka rika ba shi abinci ta hanci kuma aka sanya masa wata jaka, wadda ake amfani da ga masu larurar da ba sa iya tsugunnawa don yin bahaya da kansu.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Adélio Bispo de Oliveira told investigators he was acting “on God’s orders”

Mista Bolsonaro, wanda ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Brazil ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara, dan siyasa ne mai janyo rarrabuwar kai wanda wasu masharhanta ke kwatanta shi da Donald Trump na Amurka.

Adélio Bispo de Oliveira, a bangare guda kuma mai goyon bayan siyasar kawo sauyi ne da ke sukar lamirin Mista Bolsonaro, har ma yana wallafa sakwanni a shafukansa na Facebook don yin watsi da manufofin dan siyasar.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...