Shin kun san kasar da zubar da ciki ya fi haihuwa yawa?

Realistic looking baby dolls.

Hakkin mallakar hoto
PAARISA

Piia mazauniyar kasar Greenland ce, mai shekaru 19 inda ta shaida wa BBC cewa ”mu a kasarmu ba ma tababa wajen maganar zubar da ciki, muna yi ne a bayyane, na tuna lokacin da nake ba kawayena da ‘yan uwana labarin lokacin da na taba yi.”

Ta zubar da ciki sau biyar a shekaru biyu

Matsashiyar ta bayyana cewa ”ina amfani da kariya domin hana daukar ciki, amma wani lokaci ina mantawa. A halin yanzu ba zan iya haihuwa ba, sakamakon ina shekarar karshe a makaranta.”

Tun 2013, an samu kusan haihuwa 700 da kuma zubar da ciki 800 a duk shekara kamar yadda kiddidigar gwamnati ta bayyana.

Amma me ya sa ake yawan zubar da ciki a kasar Greenland?

Hakkin mallakar hoto
CHRISTIAN KLINDT SOELBECK

Image caption

A babban birnin kasar Greenland, dalibai na kiran Laraba a matsayin ranar zubar da ciki

Karancin tsangwama

Greenland ita ce kasa mafi girma da ke kan tsibiri me yawan mutanen da ba su wuce 55,000 ba kamar yadda kasar ta fitar da kididdigar yawan mutanenta a 2019.

Sama da rabin matan da ke daukar ciki a kasar na zubar da cikinsu. Wannan na nufin a kasar mata 30 cikin 1000 na zubar da cikinsu.

Idan za a kwatanta da kasar Denmark, mata 12 cikin 1000 ke zubar da ciki kamar yadda jami’an kasar suka bayar da kididdiga.

Duk da cewa Greenland kasa ce mai cin gashin kanta, kasa ce da ta dogara kan kasar Denmark.

Matsin tattalin arziki, karancin muhalli da kuma karancin ilimi

Wadannan abubuwan na bayar da gudummawa wajen yawaitar zubar da ciki a kasar, amma hakan ba zai zama hujja ga kasar da ke bayar da magungunan tazarar haihuwa ko kuma takaita iyali kyauta ba.

A kasashe da dama da zubar da ciki kyauta ne kuma gwamnati ta halasta hakan, masu yin hakan na fuskantar tsangwama.

A kasar Greenland, mata da yawa ba su damu ba; ba su kallon cikin da ba a bi ka’ida wajen daukarsa a matsayin abin kunya ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Duk da cewa Denmark na tallafawa Greenland da kudi, Greenland na da majalisar dokokinta

Ranar zubar da ciki

Amma me ya sa ake daukar cikin da ba a bukata?

Piia ta bayyana cewa ”Kawayena da dama sun taba zubar da ciki, mahaifiyata ta zubar da ciki sau uku kafin ta haife ni da kanina.”

Wata mai gudanar da bincike kan digirin-digirgir din da take gudanarwa a Jami’ar Roskilde a Denmark ta bayyana cewa ”dalibai a Nuuk babban birnin Greenland na zuwa asibitin wayar da kai kan jima’i wacce suke kira ‘ranar zubar da ciki.”

Piaa ta ce ”a Greenland, muhawara kan zubar da ciki ba wai wani abin tattaunawa ba ne ko kuma abin kunya, haka ma saduwa kafin aure ko kuma samun ciki ba tare da an shirya ba.”

Hakkin mallakar hoto
Media for Medical

Image caption

Greenland na baya rda magungunan tazarar haihuwa kyauta amma mata da dama ba su amfani da su.

Hanyoyin tazarar haihuwa kyauta

Piia ta bayyana cewa ”magungunan tazarar haihuwa kyauta ne kuma ba su da wuyar samu amma wasu daga cikin abokaina ba su amfani da magungunan.”

Stine Brenoe malamar asibiti ce da ke aiki bangaren haihuwa a kasar Greenland kuma ta dade tana bincike kan zubar da ciki inda ta bayyana cewa:

”Kashi 50 cikin 100 na matan da na yi bincike a kansu sun san da irin wadannan magunguna amma sama da kashi 85 cikin 100 ba sa amfani da su ko kuma suna amfani da su ba ta hanyar da ta da ce ba.”

A bincken da Turi Hermannsdottir ta gudanar, ta bayar da dalilai uku da suka sa mata ba su cika amfani da irin wadannan magunguna ba a Greenland.

”Na farko mata masu son haihuwa, abu na biyu matan da suke cikin kuncin rayuwa da ko kuma wadanda rikici ya daidaita na iya mantawa ba su sha irin wadannan magunguna ba, abu na karshe shi ne idan namiji ya manta bai saka kwaroron roba ba.

Hakkin mallakar hoto
Sean Gallup

Image caption

An halasta zubar da ciki a Greenland a 12 ga watan Yunin 1975

Cin zarafi da gudun rikici

A wani lokacin, mata na zubar da ciki idan an ci zarafinsu ta hanyar fyade suka samu cikin ko kuma suna zubar da ciki idan suna tsoron ta so da yaro a gidan da ake rikici.

Lars Mosgard wanda wani likita ne da ke wani karamin gari da ke kudancin Greenland ya bayyana cewa ” zubar da ciki ya fi barin yara kara zube suna gararamba,”

Rikicin cikin gida abu ne da yake yawan faruwa a Greenland- cikin yara 10 ana samun yaro daya da ya ga mahaifiyarsa ta fada cikin rikicin cikin gida kamar yadda kungiya ta bayyana.

Su ma yaran na fuskantar shiga rikici irin wannan.

Jami’ar gwamnatin kasar mai kula da yaki da cin zarafi Ditte Solbeck ta bayyana wa wani gidan rediyo cewa ”kashi daya bisa uku na manya da ke kasar sun taba fadawa rikici a lokutan da suke yara.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Karancin ilimi dangane da tazarar haihuwa

Duk da cewa magungunan tazarar haihuwa kyauta ne kuma ba su da wuyar samu, wannan ba shi ke nufin cewa ana amfani da su ba.

”Ban dade da sanin cewa akwai wani magani mai suna ”morning pill” ba sai watan da ya gabata, bana tunanin kowa ne ya san da maganin,” kamar yadda Piia ta shaida wa BBC.

”Mahaifiyata ba ta taba mani magana kan lafiyata ba ta bangaren da ya shafi jima’i, na samu ilimi kan jima’i ne a makaranta kuma akasari ta hanyar kawayena.”

Gidaje da dama ba su tattauna wa kan jima’i domin suna ganin hakan kamar wani abu mai wahala ne kamar yadda wani bincike ya nuna.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Zubar da ciki kyauta

Wasu na bayar da shawarwarin cewa ya kamata kasar Greenland ta daina bari ana zubar da ciki kyauta inda suke cewa a rinka karbar kudi a duk lokacin da aka zubar da ciki.

Wasu kuma na cewa yawan zubar da cikin da matan ke yi ba shi da alaka da wai don zubar da ciki kyauta ake yinsa a asibiti.

A kasar Denmark- inda nan ma kyauta ne zubar da ciki – yawan masu yin hakan ba yawa da kusan mata 12 cikin 1000.

Wani Likita na kasar Norway Johanne Sundby wanda ya taba aiki a Greenland ya bayyana cewa bai kamata a ce za a rinka biyan kudin zubar da ciki ba saboda hakan zai bayar da dama a bude wuraren bogi da za a rinka zubar da ciki ba kan ka’ida ba.

Hakkin mallakar hoto
Baby dolls

Shirin bebin roba

Bincike ya nuna cewa matasa a Greenland na fara jima’i ne a tsakanin shekara 14 zuwa 15 inda binciken ya ce kashi 63 cikin 100 na ‘yan shekara 15 a kasar na jima’i a kai a kai.

A wannan dalilin ne ya sa gwamnatin kasar ta fito da samfarin wata bebin roba wacce aka yi da hadin gwiwar makarantun kasar domin nuna illar yin jima’i a kananan shekaru ga yara.

Wannan shirin an tsara shi ne domin rage yawan samun cikin da ba a shirya ba da kuma rage yada cututtuka da kuma kara wayar da kai kan amfani da hanyoyi da magungunan tazarar haihuwa.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...