Shin gaske ne an fara takardar yarjejeniyar aure a Kano? | BBC Hausa

Kano

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Takardar yarjejeniyar da take ta yawo a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya musamman Whatsapp ta janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ke ganin takardar tamkar yin wasa da aure ne.

Yarjejeniyar dai mai taken ‘Takardar Yarjejeniya Kafin Aure’ na dauke na alkawari tsakanin miji da mata, inda mijin ya sha alwashin yin duk wani abun kyautatawa ga maryar tasa kamar haka:

  • Ciyarwa
  • Tufatarwa
  • Ilimantarwa
  • Mutumtawa
  • Kula da lafiya

Daga bangaren amarya kuma, ita ma akwai wurin da aka ware mata na sa hannu domin rantsuwa kan abubuwa kamar haka:

  • Kyale ango ya kara aure
  • Rashin cutar da shi ta hanyar amfani da makami ko guba

A karshen takardar ne kuma aka ware layuka guda tara domin sa hannun waliyan amarya da na ango da kuma alkali da da DPO na ‘yan sanda na karamar hukuma.

Ga dai yadda aka tsara takardar;

Hakkin mallakar hoto
Whatsapp

Image caption

Takardar yarjejeniyar aure da ke yawo a kafafen Soshiyal Midiya

Daga ina takardar ta fito?

Har kawo yanzu za a iya cewa ba a san daga inda wannan takarda ta fito ba kasancewar babu wani tambari da ke nuna wurin da ta fito.

Watakila wasu mutanen kan iya tinanin cewa wannan takarda ta fito da kotunan da ke jihar Kano ne sakamakon yadda aka saba duk wata takardar yarjejeniya ko rantsuwa irin wannan na fitowa ne daga kotu.

Tuni dai kotunan jihar ta Kano suka yi watsi da wannan takardar inda suka ce su ma ganin ta suka yi kamar kowa.

Mai magana da yawun kotunan jihar, Jibo Baba Ibrahim ya shaida wa BBC cewa takardar ta yi kama da ta labaran jabu ko kuma na kanzon kurege.

Me ya janyo yada takardar jabun?

Mai yiwuwa irin yadda mata kan yi amfani da makami ko kuma guba, a kan mazajensu a baya-bayan nan a Arewacin Najeriya ne ya janyo mutane suka fara yin raha.

An samu yanayin da mai gida ya yi zargin matarsa ta daba masa wuka, inda ita kuma matar ta yi zargin cewa yana yawan jibgarta ne.

Akwai irin wadannan shari’o’in masu yawan gaske dai a kotu, inda ma’auratan kan zargi juna da kokarin kisa.

Duk da cewa wannan takarda ba ta sahihanci, amma alamu na nuni ga irin bukatar da jama’a ke da ita na samun wata hanyar da za ta kawo karshen badakalar da ke yawan faruwan tsakanin ma’aurata.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...