Rahotanni daga Tudun wadan Kaduna na cewa shahararren malamin Izalar nan da yayi suna wajen wa’azin sunnah Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya sha dakyar a wajen wasu fusatattun ‘yan Darikar Tijjaniya dake Tudun Wada Kaduna.
Shedun gani da ido sun tabbatarwa wakilin mu cewa lamarin ya farune da yamma a daidai lokacin da shehin malamin ke gabatar da Tafsirin sa a masallacin ‘yan Lilo dake unguwar Tudun Wada Kaduna.
Wasu fusatattun matasan suka nufi malamin musuluncin dauke da sanduna da sauran muggan makamai a hannun su, sai dai kuma dakyar jami’an tsaron ‘yan sanda da Civil defence da ‘yan kato da gora suka taushi matasan su hana su karasawa jikin malamin.
Da yake zantawa da wakilin mu, wani daga cikin jami’an tsaron ‘yan sandan wajen da al’amarin ya faru, ya ce: “Da Allah bai sa jami’an tsaro na wajen ba da an ji mummunan labari domin matasan sun matukar fusata da yadda suka ce Kabiru Gombe tunda ya fara Tafsirin sa na wannan shekarar babu abinda yake karantarwa sai kiran sunan malamin su Sheikh Dahiru Usman Bauchi yana kafirta shi.”