Sergio Ramos ya cika shekara 14 a Real Madrid

Sergio Ramos

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kyaftin din tawagar Real Madrid Sergio Ramos ya cika shekara 14 a Santiago Bernabeu.

Dan wasan mai tsaron baya an gabatar da shi gaban magoya bayan Real a Bernabeu ranar 8 ga watan Satumbar 2005.

Ramos ya dade da karbar ragamar kyaftin din Madrid, kuma yana kaka ta 14 a Real, bayan nasarorin da ya samu, kuma yana kan ganiyarsa kawo yanzu.

Kwana biyu tsakanin da aka gabatar da shi gaban magoya baya ne ya fara buga Madrid wasa a karawa da Celta Vigo kuma a Bernabeu.

Kawo yanzu ya yi wa Real wasa sama da 609, shi ne na hudu a jerin wadan da suka yi a Real wasannin da yawa bayan Santillana mai 645 da Sanchís mai 710 da Casillas mai 725 da kuma Raúl da ya buga wa Madrid karawa 741.

Haka kuma mai tsaeron bayan ya ci kwallo 84 a kaka 14 da ya yi yana buga wa Real Madrid tamaula.

Akwai kwallaye na raba gardama da ya ci wa Real ciki har da wadda ya zura a raga a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League a 2014 da kuma 2016.

Haka kuma da wadda ya ci a UEFA Super Cup a 2016 da kuma a kofin duniya na Zakarun nahiyoyi da ya ci a 2014 da 2018.

Ramos ya lashe kofi 20 a Real da suka hada da Champions League hudu da Club World Cup hudu da UEFA Super Cup uku da LaLiga hudu da Copas del Rey biyu da kuma Spanish Super Cup uku..

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...