Saura wata daya ya rage a buga Maradona Cup

Diego Maradona

Asalin hoton, Getty Images

Ranar 14 ga watan Disamba za a buga Maradona Cup, tsakanin Barcelona da Boca Junior, don tunawa da Diego Armando Maradona.

Za a yi wasan a Saudi Arabia a birnin Riyadh, bayan da tsohon kyaftin din tawagar Argentina ya buga wa kungiyoyin biyu tamaula.

Maradona wanda ya mutu ranar 25 ga watan Nuwambar 2020, ya fara taka leda a Turai a Barcelona daga 1982 zuwa 1984 da buga mata karawa 58.

Ya kuma lashe kofi uku a kungiyar ta Sifaniya da suka hada da Copa del Rey da Spanish Super Cup da kuma Spanish League Cup.

Maradona ya buga wa Boca Junior a kakar 1981/82 da lashe Metropolitano Championship da kai kungiyar Libertadores Cup.

Ya sake komawa kungiyar daga 1995 zuwa 1997, kaka biyu da ya buga tamaula daga nan ya yi ritaya daga taka leda.

Barcelona da Boca Juniors sun fafata a tsakaninsu sau 10, karawar karshe da suka yi ita ce a Joan Gamper Trophy a 2018, inda Barca ta yi nasara da ci 3-0.

Wannan ne karo na biyu da Barcelona za ta fafata a Saudi Arabia, bayan da ta kara a Spanish Super Cup a 2020, za kuma ta kara buga wasanni a gasar a Janairun 2022.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...