Saudiyya ta zamanantar da jifan shedan | BBC Hausa

Jifan Jamrah na daga cikin muhimman ayyukan hajji

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jifan shedan dai na daga cikin muhimman ayyuka na aikin Hajji

Kasar Saudi Arabiya ta shigo da tsari na zamani wajen jifan jamrori uku da ke Muna (wato jifan shedan), wanda akan gudanar bayan hawan Arfa.

Kasar ta dauki wannan mataki ne domin lura da zirga-zirgar mahajjata tare da tabbatar da bin doka domin kare afkuwar turmutsitsi a aikin hajjin shekara ta 2019.

A watan Satumban shekara ta 2015, an kiyasta cewa turmutsitsin da aka samu a wurin jifan shedan ya haifar da mutuwar mutum kimanin 2000.

Yawan mutanen da aka rasa a wannan lokaci shi ne mafi muni a tarihin aikin hajji da Musulman duniya ke yi a kasar ta Saudiyya.

Wakilin hukumar alhazai ta Najeriya a Saudiyya, Tanko Aliyu, ya ce bukatar samar da wannan sabon tsari ya taso ne ganin cewa an sha samun matsaloli wurin jifan shedan a shekarun baya.

Inda a wasu lokutan wasu alhazan kan bace a lokacin jifan.

Jifan shedan dai na daga cikin muhimman ayyuka na aikin hajji.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Tanko Aliyu na cewa, za a rinka kai alhazan Najeriya zuwa wurin jifa kungiya-kungiya, a lokuta daban-daban da za su gudanar da nasu jifan.

Sannan kuma an tanadar da hanya ta musamman wadda alhazan Najeriya za su bi zuwa wurin jifa, kasancewar Najeriya ce ke da kashi daya cikin uku na alhazai bakaken fata da za su gudanar da aikin na bana.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...