Samuel Eto’o: Tsohon dan kwallon Barcelona zai iya takarar shugabancin kwallo a Kamaru

Samuel Eto'o
Samuel Eto’o ya ci Æ™wallo 56 a wasa 118 da ya yi wa Kamaru

An bai wa tsohon dan kwallon Barcelona, Samuel Eto’o damar tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasar Kamaru – Fecafoot.

‘Yan takara shida aka amince su tsaya takara cikin har da shugaban hukumar mai ci a yanzu Seidou Mbombo Njoya a zaben da zai gudana a ranar 11 ga watan Disamba.

Shi ma wani tsohon dan kwallon Kamaru, Jules Denis Onana an bashi damar shiga takarar amma kuma kwamitin tantancewa bai amince wa Emmanuel Maboang Kessack ya shiga takarar ba.

Sauran ‘yan takarar da za a fafata da su, sun hada da Crepin Soter Nyamsi, Justin Tagouh da kuma Zacharie Wandja.

Eto’o, mai shekaru 40, a cikin watan Satumba ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar a Kamaru duk da cewa an tayar da jijiyar wuya saboda yana da shaida zama dan wata kasar ban da Kamaru.

Eto’o, wanda ya murza leda a Inter Milan da Chelsea, ya samu takardar shaida zama dan kasar Spaniya ne lokacin da yake buga kwallo a Barcelona.

More News

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...