Sami Khedira zai yi ritaya a karshen kakar bana

Sami Kheriara

Asalin hoton, Sami Khedira

Wanda ya taba lashe kofin duniya a tawagar kwallon kafar Jamus, Sami Khedira ya sanar zai yi ritaya a wasan karshe da Hertha Berling za ta buga ranar Asabar.

Mai shekara 34 ya yanke wannan shawarar, bayan wata uku da ya koma taka leda a Hertha daga Juventus wadda ya lashe Serie A biyar a kungiyar.

Ya lashe kofi 14 jumulla a kungiyoyin da ya buga wa kwallon kafa har da Champions League da La Liga da ya ci a Real Madrid da Bundesliga a Stuttgart.

Khedira ya yi jinyar tiyata da aka yi masa kan karancin bugun zuciya a Juventus a 2019, daga baya ya koma taka leda ya kuma lashe kofi biyu a Italiya daga nan ya je Jamus.

Khedira zai yi ritaya ne mako guda da ta tabbata cewar Hertha za ta ci gaba da buga Bundesliga a badi, bayan da ta tashi ba ci da Cologne a ranar Asabar da ta gabata.

Ya yi wa Hertha wasa takwas, kuma na karshe da zai buga wa kungiyar shi ne ranar Asabar da Hoffenheim a gasar Bundesliga na karshe a kakar bana.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...