Salon yakin Koriya ta Arewa da karfin soja | BBC Hausa

Koriya

Duk da manyan taruka biyu da ganawar da aka yi kan iyakar Koriya, babu tabbas a game da tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Za mu yi bitar rikicin da ke barazanar haddasa yakin nukiliya a wasu lokuta.

Dalilin Koriya ta Arewa na kera makamin nukiliya

Bayan yakin duniya na biyu tsibirin Koriya ya rabu. Koriya ta Arewa ta kafa tsarin gwamnatin kama-karya.

Sakamakon wariya da kasashen duniya suka nuna mata, kasar ta zabi amfani da makamin nukiliya a matsayin kariya daga kasashen duniya da ke neman yakar ta.

Za ta iya kai hari da nukiliya?

Kasar ta yi gwajin nukiliyarta akalla sau shida.

Koriya ta Arewa ta yi ikirarin kera bam din nukiya da bai wuci girman makami mai cin dogon zango ba, duk da cewa ba’a tabbatar da hakan ba. Masana sun ce kasar na da makami mai linzami da ke iya kaiwa Amurka.

Ta kuma yi da’awar kera bam din Hydrogen da za ta iya amfani da rokkoki wurin harbawa. Ana tunanin a 2018 kasar ta kera makami mai tafiya a karkashin ruwa.

Yaya aka fara tattaunawar?

Bayan watanni barazanar da bangaraorin ke wa juna na ta karuwa, a watan Janairun 2018 shugaba Kim ya ce “kofarsa a bude take a tattauna”.

Mista Trump ya karbi tayin, sannan ya yi watsi da sharadin da ya gindaya cewa sai Koriya ta Arewa ta fara lalata makamanta na nukiliya.

12 ga watan Yunin 2018, Mista Trump ya zama shugaban Amurka mai ci na farko da ya hadu da shugaban Koriya ta Arewa.

Shugabannin biyu sun rattaba hannu a yarjejniyar “kammala lalata makaman nukiliyan tsibirin Koriya”. Sai dai kuma babu cikakken bayani.

Rashin daidaito ya cigaba

Daga nan ba wata nasarar a zo a gani. Amurka na neman Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na makaman nukiliya. Pyongyang kuma na so a bi daki-daki domin sassauta takunkumin da aka kakaba mata.

Kasashen sun sake yin babban taro a Hanoi ranar 28 ga watan Fabrairun 2019. Taron ya watshe saboda bukatar Koriya ta Arewa na a janye takunkimin da aka sa mata.

A hakan kuma Pyongyang ta sake gwajin makamai, abin da ake gani kokari ne na karin matsin lamba ga Amurka.

Shugabannin sun yi taro a iyakar Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu ranar 30 ga watan Yuni inda Donald Trump ya samu shiga cikin Koriya ta Arewa na dan lokaci.

Pyongyang ta kuma yi gudanar da gwajin makamai a matsayin jan kunne, yayin da Koriya ta Arewa da Amurka ke shiring atisayen gwajin karfin soji a watannin Yuli da Agusta.

Wata tattaunawa da aka yi a Oktoba ta gaza kawo sabon cigaba.

Duk da raguwar tayar da jijiyoyin waya tsakaninta da Koriya ta Kudu, babu alamar cewa Pyongyang ta rage karfinta na soji.

Karfin makamai da sojin Koriya ta Arewa

A 2017 Koriya ta Arewa ta yi gwaje-gwajen makamai da dama domin nuna yadda take kara fasaharta na aikin soja ke bunkasa cikin sauri.

Anan ganin Makamin Hwasong-12 da ta kera mai cin zangon kilomita 4,500 zai ba Koriya ta Arewa damar kai wa sansannin sojin Amurka da ke tsibirin Guam hari.

Hwasong-14 da ta kera daga baya ya nuna karin karfin sojoan Kasar. Kwararru sun ce Hwasong-14 zai iya cin zangon kilomita idan aka harba daga sama.

Hwasong-14 shi ne cikakken makami mai linzami mai tsallaka wata nahiya zuwa wata na farko da Pyongyang ta mallaka kuma yana iya kaiwa New York na kasar Amurka.

Daga baya kasar ta yi gwajin Hwasong-15, wanda ya kai bisan kilomita 4,500 a sararin samaniya – ninki 10 na tashar binciken sararin samaniya ta duniya.

Yana iya cin nisan kilomita 13,000 idan aka harba shi daga shimfidadden wuri. Hakan na nufin zai iya kaiwa kowane yanki na nahiyar Amurka.

Sai akwai masu shakkun ko makamai masu linzamin na cin zangon da kasar ke ikirari. Akwai kuma kokwanaton ko kasar na da cikakken kwarewar harbo duk abin da ta kai wa hari.

A 2019 Koriya ta Arewa ta yi gwajen wasu makamai masu gajeren zango, a matsayin karin gargadi ga atisayen da sojojin makwabciyarta Koriya ta Kudu da sojijin Amurka za su yi a watannin Yuli da Agusta.

Da alamun a Oktoba Pyongyang ta kera wani sabon makami, bayan ta yi gwajin wani makami mai linzami da za’a iya harbawa daga jirgi mai tafiya a karkashin ruwa.

Iya harba makami mai linzami daga jirgi mai tafiya a karkashin ruwa ya alamta karuwar karfin kai harin Koriya ta Arewa da kuma wuyar gano ta inda za ta harba makaman da za su iya kaiwa Hawaii na kasar Amurka, ya rage matsalar kasar na karancin jirage.

Nasarorin da Koriya ta Arewa ta yi a gwajin makaman da ta yi ya sa ake kokarin gano yadda shirin kasar na kera makami mai linzami ya bunkasa da sauri. Masu sharhi na zargin Pyongyang ta fasahar ne ta haramtacciyar hanya daga kasashin Rasha da Ukraine.

[ad_2]

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...