Sakin ‘yan Taliban ya jawo ce-ce-ku-ce | BBC Hausa

Shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Ashraf Ghani, yana da ra’ayin ganin an sasanta da Taliban don kawo karshen rikici a Afghanisatn da ma yankin gaba daya

Ana ta suka da caccakar shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani a kan amincewa da ya yi a saki fursunonin yaki yawanci ‘yan kungiyar Taliban a matsayin wata karramawa ta albarkacin Idin karamar sallah.

Shugaban wanda wa’adinsa a matsayin shugaban kasa ya kare a watan da ya wuce, ya bayyana matakin ne a ranar Talata, sai dai bai fadi su waye fursunonin ba da kuma irin laifukansu ba.

Da yake bayar da cikakken bayani game da wannan shiri na afuwa ga ‘yan sarkar, Shugaban na Afghanistan, Ashraf Ghani, ya ce matakin na daga cikin abubuwan da suka amince a zaman tattaunawa na tabbatar da zaman lafiya wanda aka shirya yi da kungiyar Taliban.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Mayakan Taliban na ikirarin kafa daular Musulunci ne, inda suka fara gwagwarmaya a Afghanistan a 1996

To sai dai wannan mataki na gwamnatin na sasantawa da wanzar da zaman lafiya da masu tayar da kayar bayan, albarkacin Idin, ya haifar da takaddama tare da cin karo da suka tun daga bayyana shi, abin da ya sa ake ta kira da gwamnatin ta yi watsi da shi.

Masu nuna shakku ko tababa da dari-dari, da kuma masu suka a game da dabarar, suna nuna cewa su kam ba su ga dalilin sakin mayakan ba, alhalin kungiyar ‘yan Taliban din na ci gaba da kai hare-hare.

‘Yan takarar shugabancin kasar da dama, na cewa Mista Ghani ba shi ne shugaban Afghanistan ba na halaliya a yanzu, saboda haka babu wani dalili ko iko da yake da shi da zai aiwatar da wani muhimmi ko babban hukunci kamar wannan.

Sai dai Mista Ghani, ya kafe a kan ra’ayinsa na ci gaba da zama a kan mulki, har sai an yi sabbin zabuka, amma kuma ‘yan hamayya sun ce atafau hakan ba za ta sabu ba.

A kan hakan sun yi barazanar bijirewa tare da yin gargadin tayar da zaune tsaye a siyasar kasar ta Afghanistan, idan ya ci gaba da zama a kan mulki.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...