Connect with us

Hausa

Sabuwar takaddama tsakanin Jamus da Rasha Labarai

Published

on

Jamus ta dakatar da saukar jiragen Rasha a cikin kasarta, a wani mataki na ramuwar gayya in ji wata sanarwa da ma’aikatar sufurin kasar ta fitar.

Matakin dai na zuwa ne bayan da kamfanin jiragen samar kasar ta Jamus na Lufthansa ya soke tashi zuwa kasar, sakamakon rashin samun izini daga Rashar.

Sai dai kawo yanzu ma’aikatar sufuri da ofishin jakadancin Jamus na cigaba da tattaunawa da hukumar sufurin jiragen sama ta Rasha domin lalubo bakin zaren. Kimanin jirage bakwai ne abin ya shafa daga ranar Talata da wannan Larabar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending