Sabuwar shigar zamani ta bulla a Kongo

An jima da sanin wasu mazauna tagwayen manyan biranen Kongo na Brazzaville da Kinshasa a kan soyayyarsu ga kaya masu ado na kwalisa musamman ma al’ummar al-Sape

Wadannan hotunan na Tariq Zaidi sun bayyana yadda al’ummar ta al-sape suka sake kawata shigarsu dai dai da zamani.

Wani yaro mai shekara takwas, dan wani shahararren mutum mai suna Fiston Mahata kenan dake birnin Kinshasa wanda na daya daga cikin masu wakiltar sabuwar shigar zamanin.

A gefen Kogin Congo a Brazzaville, Okili Nkoressa mai shekaru 10, dake tsakiya, yana amfani da hanyoyin da ba su da shara sosai wajen yin tafiya mai jan hankalin mutane.

“Kayan da na fi so shi ne na Yves Saint Laurent, kwat ce irin wadda yake sanye da ita a wannan hoto.

A wannan hoto dake sama yana tare ne da wasu tsoffin al’ummar al-Sape, daga hagu wata ‘yar kasuwa ce mai shekaru 52 mai suna Ntsimba Marie Jeanne, da kuma wani mutum mai suna Judith Nkoressa a hannun dama.

Shima mahaifin Severin Mouyengo dan kungiyar ne, ”Ina dandasa irin wannan kwalliya kullum”, takan sa in manta duk wata damuwa” in ji mutumin mai shekaru 62 a duniya.

”Tana sanya nishadi ga kowa, banga dalilin da zai sa wani ya kalli wannan shiga a matsayin abar tada hankali ba”, a cewarsa.

Elie Fontaine, mai shekaru 45 na haihuwa wanda direban tasi ne ya ce ya fara irin shigar ne tun a shekarar 1982.

Ya ce sun ja hankalin duniya a shekarar 2014, bayan da aka watsa irin shigar tasu a wani tallan tarihi.

”Ni a guri na ado ne, sannan sana’a ce” in ji Maxime Pivot Mabanza, wanda ya shafe shekaru 36 yana yin shigar.

Perreira Franchisco mai shekaru 37 a duniya yana gyaran kwamfuta a Brazzaville, ya ce yana kallon kansa a matsayin wanda yafi kowa iya shigar.

Mata da dama na karbar shigar hannu bibbiyu, ciki kuwa har da wannan mata da ta kyafe, shekarunta 44, kuma ‘yar kasuwa ce, sunanta shi ne Ella Kiadi, kuma ta fara shigar ne tun kusan shekaru takwas da suka gabata.

Wasu daga cikin matan sun fara shigar ne tun kusan shekaru goma da suka gabata, ciki kuwa har da wannan mata da ke rike da tukunyar lofe a bakinta, shekarunta 52 a duniya.

”Kamar mutum ne wanda ke fama da cuta, don haka shan magani gare shi ya zama dole, abin da yasa nake yin shigar kenan'” in ji Nino Valentino.

Wani jami’in walwalar ma’aikata na kamfanin Gandzion mai shekara 51, shima ya shafe shekara 30 yana yin shigar.

”Cikin dukkanin kaya na wannan da nake sanye da shi na si so, ” a cewar wannan mutumi wanda birkila ne dan shekara 58 mai suna Yamea Bansimba, shekarunsa 50 yana yin shigar.

Wannan Jika ne taken da ake yi masa ke nan. Yana wannan shigar, dan shekara 28 Serge Bakama Boke da aka fi sani Jika yana matukar kaunar wannan shiga.

Wani dan yaro mai shekara 5 kacal a duniya kenan Israell Mbona, tun yana dan shekara biyu ya soma yin shigar.

Kayan nasa sun zo ne daga Scotland, sannan takalmansa Versace ne.

Dukkanin wadannan hotuna na Tariq Zaidi ne.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...