Sabon Sarkin Japan, Naruhito, ya fara mulkinsa

Naruhito and Empress Masako

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sarki Naruhito da matarsa Masako a yayin da yake jawabinsa na farko a Fadar Imperial.

Sabon Sarki Naruhito na Japan ya yi jawabinsa na fari bayan da ya dare karagar mulki, kuma yayi fatar samun farin ciki da zaman lafiya a duniya.

An gudanar da wani biki a Fadar Imperial ranar Laraba inda ya dare karagar mulkin kasar.

Wani sabon karni mai suna Reiwa – wanda ke nufin oda da tsari – ya fara kenan har karshen mulkinsa.

Mahaifinsa Akihito mai shekara 85 ya kasance sarki na farko da ya sauka daga mukaminsa ranar Talata a tsawon fiye da shekara 200.

Sarki Naruhito mai shekara 59 da haihuwa ya gode wa mahaifinsa tsohon Sarki Akihito.

“Ya gudanar da dukkan ayyukansa da sadaukar da kai na tsawon fiye da shekaru 30,” inji shi. “Ya kuma nuna tausayawa ga gajiyayyun cikin al’ummarsa. Ina son mika godiya ta musamman da jinjina a gare shi.”

Hakkin mallakar hoto
AFP PHOTO / IMPERIAL HOUSEHOLD AGENCY

Image caption

Hoton auren Sarki Naruhito da matarsa Masako sanye da tufafin gargajiya a 1993.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...